AFCON 2023: Gwamnatin Tinubu Ta Yi Wa Super Eagles Muhimmin Alkawari Saboda Kai Wa Wasan Karshe

AFCON 2023: Gwamnatin Tinubu Ta Yi Wa Super Eagles Muhimmin Alkawari Saboda Kai Wa Wasan Karshe

  • Gwamnatin tarayya ta yi alƙawarin ba tawagar Super Eagles ta Najeriya kyauta bayan ƙungiyar ta kai wasan ƙarshe a gasar AFCON 2023
  • Ƴan wasan Najeriya sun yi aiki tuƙuru a wasan kusa da na ƙarshe da ƙungiyar Bafana Bafana ta Afrika ta Kudu a ranar Laraba, inda suka samu nasara da ci 4-2 a bugun daga kai mai tsaron gida
  • Bayan nasarar, mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima, ya shaida wa ƴan wasan cewa ƴan Najeriya na alfahari da wannan rawar da suka taka

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Abidjan, Côte d’Ivoire - Gwamnatin tarayya ta yi alƙawarin ba tawagar Super Eagles ta Najeriya tukuici.

Gwamnatin za ta ba Super Eagles kyauta mai tsoka ne saboda jajircewar da suka yi wajen kai wa wasan ƙarshe na gasar cin kofin AFCON 2023 da ke gudana a Cote d’Ivoire.

Kara karanta wannan

Hedikwatar tsaro ta fadi abu 1 da za a yi don kawo karshen matsalar rashin tsaro a Najeriya

FG za ta ba Super Eagles kyauta
Gwamnatin tarayya za ta ba tawagar Super Eagles kyauta mai tsoka Hoto: @NGSuperEagles
Asali: Twitter

Nasarar Super Eagles ta faranta ran ƴan Najeriya

A cewar mataimakin shugaban ƙasan Najeriya, Kashim Shettima, gwamnatin jam'iyyar APC da al'ummar Najeriya na alfahari da nasarar da Super Eagles ta samu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wata sanarwa da aka sanya a shafin X (tsohon Twitter) na Super Eagles a safiyar ranar Alhamis, 8 ga watan Fabrairu, ta nuna cewa a yayin ziyarar da Shettima ya kai wa ƴan wasan yana tare da Gwamna Dapo Abiodun (jihar Ogun) da Gwamna Duoye Diri (jihar Bayelsa).

Sauran ƴan tawagarsa sun haɗa da ministar matasa, Jamila Ibrahim, hamshaƙin ɗan kasuwar man fetur, Wale Tinubu, wakilin hukumar FIFA, Amaju Pinnick, da shugaban hukumar ƙwallon kafa ta Najeriya (NFF), Ibrahim Gusau.

Hotunan da aka sanya sun nuna ƴan wasan da masu basu horo tare da tawagar mataimakin shugaban ƙasan cikin murna.

Kara karanta wannan

Majalisa ta waiwayi batun digiri dan Cotonou, ta dauki muhimmin mataki

Kashim Shettima Ya Shilla Cote d'Ivoire

A baya rahoto ya zo cewa mataimakin shugaban ƙasan Najeriya, Kashim Shettima ya shilla zuwa ƙasar Cote d'Ivoire domin kallon wasan da Najeriya za ta yi da ƙasar Afirika ta Kudu a wasan dab da na kusa a ƙarshe a gasar AFCON 2023.

Mataimakin shugaban ƙasar ya tafi ne domin ƙarfafa gwiwar ƴan wasan Super Eagles a wasan da za su yi da takwarorinsu na Bafana Bafana ta Afirika ta Kudu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng