AFCON: Kashim Shettima Ya Shilla Cote d’Ivoire Domin Kallon Wasan Super Eagles da Afrika Ta Kudu
- Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya bar Abuja, babban birnin Najeriya zuwa Abidjan na kasar Cote d'Ivoire
- Shettima bisa wakilcin shugaba Bola Tinubu zai halarci wasan kusa da na karshe na gasar cin kofin AFCON da za a buga tsakanin Najeriya da Afrika ta Kudu
- Ziyarar mataimakin shugaban kasa zuwa Cote d'Ivoire wani kira ne mai karfi na hadin kan kasa da goyon bayan 'yan wasanta
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima bisa wakilcin shugaba Bola Tinubu ya bar Abuja, babban birnin Najeriya zuwa Abidjan na kasar Cote d'Ivoire.
Shettima zai je kasar ne don karfafa guiwar ztawagar Super Eagles ta Najeriya a karawar da za ta yi da kasar Afrika ta Kudu a wasan kusa da na karshe na gasar cin kofin nahiyar Afirka (AFCON).
Ya wallafa sanarwar hakan a shafinsa na X inda ya bayyana cewa za a buga wasan ne a filin wasa na Stade de la Paix da ke Bouake na kasar Cote d'Ivoire a yammacin yau.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Abinda ziyarar Shettima ke nufi
Ziyarar ta mataimakin shugaban kasar za ta kara babbar alakar da ke tsakanin kwallon kafa da nuna kishin kasa a Najeriya.
Kasancewar sa a filin wasan ba wai kawai zai kara wa Super Eagles kwarin gwiwa ba ne ba, har ma ya zama wata matattara ga miliyoyin 'yan Najeriya da ke murna daga gidajensu.
Gasar AFCON ta bana ta sa Super Eagles ta kara zuwa wani sabon mataki, kamar yadda mataimakin shugaban kasar ya bayyana.
Yan Najeriya za su yi wa Super Eagles fatan Nasara
Shettima ya lura cewa da wannan ne karo na 15 da suka buga wasan kusa da na karshe, Najeriya ce ke rike da kambun mafi yawan wasanni a wannan mataki.
Ziyarar mataimakin shugaban kasa zuwa Cote d'Ivoire wani kira ne mai karfi na hadin kan kasa da goyon bayan 'yan wasanta.
A yayin da Super Eagles ke shirin tunkarar wasan daf da na kusa da na karshe, an yi kira ga ‘yan Najeriya a fadin duniya da su yi wa kungiyarsu kyakkyawan fata.
Kalli bidiyon a kasa:
Asali: Legit.ng