AFCON: Cikakken Sunayen ’Yan Wasan Najeriya 5 da Suka Fi Zura Kwallaye a Tarihin Gasar
Tawagar kungiyar kwallon kafa ta Najeriya, Super Eagles ta samu tsallakawa zuwa zagayen kusa da na karshe wato sami fainal bayan doke kasar Angola.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Najeriya ta yi nasara kan kasar Angola da ci daya mai ban haushi a ranar Juma’a 2 ga watan Faburairu.
Jerin 'yan wasan 5 a Najeriya
Wannan shi ne karo na 16 da kasar ta samu damar zuwa matakin sami fainal bayan nasarori a sauran wasannin baya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Legit Hausa ta jero muku ‘yan wasa biyar da suka fi kowa shan kwallaye a gasar AFCON ga Najeriya.
1. Rashidi Yekini
Marigayi Rashidi Yekini shi ne ya fi kowa shan kwallaye ga kasar Najeriya inda ya jefa kwallaye 13 a gasar.
Yekini har ila yau, shi ne dan wasan da yafi kowa shan kwallaye a kasar baki daya da kwallaye 37.
2. Austin Jay-Jay Okocha
Okocha shi ne na biyu bayan ya sha kwallaye bakwai a gasar AFCON inda ya fara shan kwallo a 2000, cewar Soccernet.
Okocha ya zama dan wasan da ya fi kowa bajinta a gasar Tunisia 2004 tare da shan kwallaye hudu a gasar.
3. Segun Odegbami
Segun shi ne dan wasa na uku da yafi kowa shan kwallaye a kasar da kwallaye shida.
A wasansa na farko ya sha kwallaye uku a shekarar 1978 a gasar da aka gudanar a kasar Ghana.
4. Julius Aghahowa
Aghahowa shi ma ya sha kwallaye har guda shida a gasar AFCON da ya buga a rayuwarsa.
5. Odion Ighalo
Ighalo shi mutum na biyar a jerin wadanda suka fi kowa shan kwallaye a gasar AFCON, cewar The Nation.
Dan wasan ya sha kwallaye biyar inda ya zama wanda ya fi kowa shan kwallaye a gasar da aka yi a Masar a shekarar 2019.
Osimhen ya ji rauni a gasar AFCON
Kun ji cewa akwai hasashen cewa zai yi wahala Victor Osimhen ya buga wasa da kasar Afirka ta Kudu.
Daga bisani likitoci sun yi kwakkwaran bincike inda suka tabbatar Osimhen zai iya buga wasan su da kasar Afirka ta Kudu.
Asali: Legit.ng