AFCON 2023: Jerin Lokutan da Najeriya Ta Doke Afrika Ta Kudu Tun Daga Shekarar 1992

AFCON 2023: Jerin Lokutan da Najeriya Ta Doke Afrika Ta Kudu Tun Daga Shekarar 1992

  • Najeriya za ta sabunta adawarta da Afirika ta Kudu a ranar Laraba lokacin da Super Eagles za ta kara da Bafana Bafana ta Afirka ta Kudu
  • Tun a shekarar 1992 ƙungiyoyin biyu sun haɗu sau 14, kuma Super Eagles ta doke Afrika ta Kudu sau bakwai
  • Wasan na Laraba zai kasance karo na goma sha biyar, kuma masana da dama sun yi hasashen Najeriya za ta iya doke takwararta ta Afirka ta Kudu a wasan

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Abidjan, Cote d'Ivoire - Super Eagles ta Najeriya za ta fafata da Bafana Bafana ta Afirka ta Kudu a wasan dab da na ƙarshe a gasar cin kofin nahiyar Afirika (AFCON) da ake ci gaba da yi.

Kara karanta wannan

AFCON 2023: Hanyoyi 3 da tawagar Najeriya za ta iya doke Afrika ta Kudu a wasan kusa da na karshe

Ƙasashen biyu za su fafata ne a filin wasa na Stade Bouake da ke ƙasar Ivory Coast a ranar Laraba, 7 ga watan Fabrairu da ƙarfe 6:00 na yamma.

Lokutan da Najeriya ta doke Afirika ta Kudu a tarihi
Najeriya za ta fafata da Afirika ta Kudu a wasan dab da na karshe a gasar AFCON 2023 Hoto: Super Eagles, Bafana Bafana
Asali: Twitter

Abin sani kan Najeriya vs Afirika ta Kudu

An dai yi ta cece-kuce da hasashe kan yadda wasan zai kaya tsakanin ƙasashen biyu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai kuma, sakamakon fafatawar da aka yi tsakanin Najeriya da Afirka ta Kudu tun a shekarar 1992, ya nuna cewa Super Eagles ta doke Bafana Bafana sau bakwai a karawa 14 da suka yi.

Sau biyu kawai ƴan wasan Afrika ta Kudu suka doke Super Eagles, yayin da ƙasashen biyu suka buga canjaras sau biyar.

Bashir Ahmad, tsohon mai taimaka wa tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ne ya bayyana haka.

Najeriya vs Afirika ta Kudu a tarihi

Kara karanta wannan

Babbar kotu ta yanke hukunci kan buƙatar magoya bayan gwamnan PDP da ake zargi da ta'addanci

1. 10 ga watan Oktoba,1992: Najeriya 4 - 0 Afirka ta Kudu (1994 wasan neman zuwa cin kofin duniya, Legas)

2. 16 ga watan Janairu, 1993: Afirka ta Kudu 0 - 0 Nigeria (1994 wasan neman zuwa cin kofin duniya, Johannesburg)

3. 10 ga watan Fabrairu, 2000: Najeriya 2 - 0 Afirka ta Kudu (Wasan dab da na ƙarshe a gasar AFCON, Legas)

4. 31 ga watan Janairu, 2004: Najeriya 4 - 0 Afirka ta Kudu (Wasan ƙarshe na AFCON, Monastir, Tunisia)

5. 17 ga watan Nuwamba, 2004: Afirka ta Kudu 2 - 1 Najeriya (Wasan sada zumunta, Durban)

6. 1 ga watan Yuni, 2008: Najeriya 2 - 0 Afirka ta Kudu (Neman zuwa gasar cin kofin duniya na 2010, Abuja)

7. 6 ga watan Satumba, 2008: Afirka ta Kudu 0 - 1 Najeriya (Neman zuwa gasar cin kofin duniya na 2010, Port Elizabeth)

8. 14 ga watan Agusta 2013: Afirka ta Kudu 0 - 2 Najeriya (Wasan sada zumunta, Johannesburg)

Kara karanta wannan

AFCON 2023: Bature ya fadi makomar tawagar Najeriya a wasan da za ta buga da Afrika ta Kudu

9. 10 ga watan Satumba 2014: Afirka ta Kudu 0 - 0 Najeriya (Neman zuwa gasar cin kofin AFCON 2015, Johannesburg)

10. 19 ga watan Nuwamba 2014: Najeriya 2 - 2 Afirka ta Kudu (Neman zuwa gasar cin kofin AFCON 2015, Uyo)

11. 29 ga watan Maris 2015: Afirka ta Kudu 1 - 1 Najeriya (Wasan sada zumunta, Durban)

12. 10 ga watan Yuni 2017: Najeriya 0 - 2 Afirka ta Kudu (Neman zuwa gasar cin kofin AFCON 2019, Uyo)

13. 17 ga watan Nuwamba, 2018: Afirka ta Kudu 1 - 1 Nigeria (Neman zuwa gasar cin kofin AFCON 2019, Johannesburg)

14. 10 ga watan Yuli, 2019: Najeriya 2 - 1 Afirka ta Kudu (Wasan dab da na kusa da na ƙarshe a AFCON 2019, Cairo).

An Shirya Liyafa Don Super Eagles

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban matasan jam’iyyar APC, Dayo Israel, ya shirya wata kwarya-kwaryar liyafa domin ƙarfafa gwiwar ƴan wasan Super Eagles.

Shugaban matasan ya ce liyafar za ta haɗa kan matasan jam’iyyar APC da wadanda ba ƴan jam’iyyar ba a Abuja domin marawa tawagar Najeriya baya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng