‘Za a Gwabza’: Mai Tsare Ragar Tawagar Afrika Ta Kudu Ta Shirya Karawa da Super Eagles a Gasar AFCON

‘Za a Gwabza’: Mai Tsare Ragar Tawagar Afrika Ta Kudu Ta Shirya Karawa da Super Eagles a Gasar AFCON

  • Dan wasan tsaron raga na kasar Afrika ta Kudu ta bayyana shirinsa na tunkarar ‘yan wasan Super Eagles na Najeriya a wasan AFCON
  • Dan wasan mai suna Williams ya bayyana hakan ne bayan da kungiyarsu ta Bafana Bafana ta yi nasa kan Cape Verde zuwa zango na biyun karshe
  • Bafana Bafana a shirye suke wajen tunkarar Najeriya da ke ci gaba da ji da kai da kwarin gwiwar lallasa kowacce kasa

Salisu Ibrahim ne babban editan (Copy Editor) sashen Hausa na Legit. Kwararren marubucin fasaha, harkar kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas

Biyo bayan lallasa kasar Cape Verde, golan Afrika ta Kudu, Ronwen Williams ya ce, a shirye suke su tunkari Najeriya a wasan AFCON.

A ranar Asabar 3 ga watan Faburairu, Afrika ta Kudu ta samu nasarar isa zango na biyun karshe bayan lallasa Cape Verde ci 2 da 1, Eurosports ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Aikin gama ya gama: Dan takarar PDP ya sha kaye a zaben cike gurbi a Yobe, an fadi wanda ya lashe

A shirye muke mu buga da Najeriya, Afrika ta Kudu
Za mu buga a gani Afrika ta Kudu da Najeriya | Hoto: @VjWale
Asali: Twitter

Bayan nasarar, dan wasan tsaron ragar ya bayyana cewa, a shirye yake ya gamu da duk wani harin da dan wasan gaban Najeriya, Victor Osimhen zai kawo a wasansu na gaba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Meye dan wasan Afrika ta Kudu ya ce?

A cewar rahoton SportsBrief, an naqalto Williams na cewa:

“Mun zai zama babban al’amari da ke tafe don haka muna bukatar kyakkyawan shiri kuma muna nan jiran kayawarmu.”

A bangare guda, tawagar Afrika ta Kudu, Bafana Bafana ce dai ta yi nasara a gasar AFCON 1996, inda ta buga wasan karshe da Najeriya.

Rahoton All Nigeria Soccer ya bayyana cewa, tawagar Afrika ta Kudu na ci gaba da shiri a daidai lokacin da Najeriya ma ke ci gaba da na ta shirin.

Akwai yiwuwar Najeriya ta ci gasar bana?

A wannan wasa, Najeriya dai na ci gaba da nuna kwazo ainun wajen tabbatar da ta dauki kofin da ya fi kowanne a Afrika.

Kara karanta wannan

AFCON 2023: Jerin kasashe 2 da Super Eagles za ta iya karawa da su a wasan kusa da na karshe

Ba wannan ne karon farko da Najeriya ke kaiwa zangon karshe na wasan ba, kasar ta sha yin hakan a baya.

To amma, hasashe na nunawa a wannan shekarar akwai alamar Najeriya ta ba da sakamakon da zai haifar da da mai ido.

Da wacce kasa Najeriya za ta hadu da ita a AFCON?

Idan baku manta ba, Super Eagles ta Najeriya ta tsallake zuwa wasan kusa da na karshe a gasar cin kofin nahiyar Afirka da ake gudanarwa a shekarar 2023.

Najeriya ta samu nasarar ne bayan da ta doke Palancas Negras ta Angola da ci 1-0 a Abidjan a ranar Juma'a 2 ga Fabrairu.

Super Eagles dai ta yi aiki tukuru domin samun nasara a kan kungiyar Palancas Negras, wadda ta bada mamaki na yadda ta kai wasan daf da na kusa da na karshe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.