NFF Ta Bayyana Dalili 1 da Zai Sanya Tawagar Super Eagles Lashe Kofin AFCON
- Ƴan Najeriya a shafukan sada zumunta sun mayar da martani daban-daban kan kalaman da hukumar NFF ta yi a baya-bayan nan game da kofin AFCON
- Masu amfani da shafukan sada zumunta sun buƙaci hukumar NFF da kada ta kawo siyasa a cikin tawagar ƴan wasan Super Eagles
- Hakan ya biyo bayan da NFF ta bayyana cewa Super Eagles za ta ɗauki kofin domin Shugaba Tinubu
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Hukumar kula da kwallon ƙafa ta Najeriya (NFF) ta danganta nasarar da Super Eagles ta samu a kan Angola a gasar cin kofin AFCON 2023 a ƙasar Ivory Coast ga shirin sabon fata na Shugaba Bola Tinubu.
Kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito, NFF ta bada tabbacin cewa tawagar Super Eagles za ta lashe kofin saboda Tinubu.
Shugaban NFF Ibrahim Gusau, wanda ya bayyana haka a Abidjan a ranar Asabar, 3 ga watan Fabrairu, ya gode wa Tinubu kan goyon bayan da ya ba shi, inda ya jaddada ƙudirin shugaban kasar na bunƙasa wasanni, musamman kwallon ƙafa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bayan nasarar 1-0 akan Angola, wanda Ademola Lookman ya ci ƙwallon, Gusau ya yaba da kalaman ƙarfafa gwiwar Tinubu ga Super Eagles.
A kalamansa:
"Da yardar Allah, na san zai ba su kyauta mai kyau, wacce ba a taɓa samun irinta ba a tarihin Nijeriya.
"Mun yi masa alƙawarin cewa za mu ba shi kofin, kuma da yardar Allah za mu yi hakan."
Ƴan Najeriya sun yi martani
Wannan iƙirari da hukumar ta NFF ta yi ya janyo cece-kuce a shafukan sada zumunta.
Kamar yadda aka saba, ƴan Najeriya sun shiga sashin sharhi kuma sun mayar da martani kan kalaman na NFF.
Ga wasu daga cikin waɗanda Legit Hausa ta tattaro:
@MalcolmInfiniti ya rubuta:
"Don Allah NFF za ku iya dakatar da wannan neman sunan? Nasarar da Super Eagles ta samu a AFCON 2023 ba shi da alaƙa da "ajandar sabunta fata" ta Tinubu. Don Allah ku cire siyasa a ƙwallon ƙafa kada ku jawo musu rashin sa'a."
@RealQueenBee__ ta rubuta:
"Kada ku kuskura ku kawo Tinubu cikin wannan zance."
@ChrisEjiofor7 ya rubuta:
"Wannan magana ta siyasa ce kuma wasan ƙwallon ƙafa wasa ne kawai, saboda wannan magana Super Eagles' na iya rasa kofin."
@chibestvalen ya rubuta a tweet:
"Ɗan wasan ƙwallon ƙafan da ake jin daɗi za ku zo ku lalata."
@Derik_more ya rubuta:
"Shin suna wasa ne don su burge Tinubu ko kuma su lashe kofin ga ƴan Najeriya?
Ƙasashen da Najeriya Za Ta Iya Karawa da Su
A wani labarin kuma, an jero ƙasashen da Najeriya za ta iya karawa da su a zagayen dab da na ƙarshe a gasar cin AFCON 2023.
Najeriya dai na iya fuskantar ƙasashen South Africa ko Cape Verde, bayan ta doke Angola a zagayen dab da na kusa da na ƙarshe.
Asali: Legit.ng