AFCON 2023: An Yi Hasashen Tawagar da Za Ta Lashe Gasar Kofin Afrika

AFCON 2023: An Yi Hasashen Tawagar da Za Ta Lashe Gasar Kofin Afrika

  • Yanzu haka Super Eagles ta Najeriya ce ke kan gaba wajen ganin ta lashe gasar cin kofin nahiyar Afirka (AFCON 2023) da ke gudana a kasar Cote D’Ivoire
  • Wannan na kunshe ne a cikin sabon hasashen da 'Opta supercomputer' ya yi bayan ficewar Senegal da Maroko daga gasar
  • Kasashe takwas ne suka samu nasarar zuwa zagayen kusa da na kusa da na karshe na AFCON wanda za a fara ranar Juma'a 2 ga watan Fabrairu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fanni n nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abidjan, Cote D’Ivoire - Kamfanin 'Opta supercomputer' ya fitar da jerin kasashen da ka iya lashe gasar cin kofin nahiyar Afirka da ake gudana bayan fitar da Senegal da Moroko.

Kara karanta wannan

Yadda ma'aikacin banki ya yi karyar 'yan bindiga sun sace shi saboda bashin naira miliyan 1.7

Senegal, wadda ake saka tsammani a kanta, ta sha kashi a zagaye na 16 a hannun mai masaukin baki, Cote D’Ivoire a bugun fanareti a ranar Litinin, 29 ga watan Janairu.

Supercomputer ya yi hasashen Najeriya za ta lashe gasar AFCON 2023
Supercomputer ya yi hasashen Najeriya za ta lashe gasar AFCON 2023. Hoto: @NGSuperEagles
Asali: Twitter

Najeriya na kan gaba a hasashen daukar kofin

Yayin da Moroko wadda ta kai wasan kusa da na karshe a gasar cin kofin duniya ta Qatar 2022 ta sha kashi hannun Afirka ta Kudu a ranar Talata, 30 ga Janairu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cikin hasashen Opta na baya-bayan nan, Super Eagles ta Najeriya ce ke kan gaba a jerin kasashen da ka iya daukar kofin da kashi 28.8% cikin dari.

Super Eagles wadda ta taba lashe kofin AFCON har sau 3, za ta kara da Angola a zagayen kusa da na kusa da na karshe a ranar Juma’a 2 ga watan Fabrairu.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun kwamushe mutum 10 da ake zargin masu garkuwa da mutane ne a jihar Akwa Ibom

Supercomputer ya yi hasashen Najeriya za ta lashe gasar AFCON 2023.
Supercomputer ya yi hasashen Najeriya za ta lashe gasar AFCON 2023.
Asali: UGC

Kasashen da ke bin bayan Najeriya

Kasar Mali mai kashi 14.7% da Cote D’Ivoire da ke da kashi 13.5% ne ke bayan Najeriya a jerin kasashe uku da suka fi son lashe gasar AFCON ta 2023.

Kasa ta hudu a jerin mau son daukar kofin a ranar 11 ga watan Fabrairu ita ce kasar Kongo da ke da kashi 9.4% cikin dari yayin da Cape Verde ke da damar daukar kofin da kashi 8.8%.

Sauran sun hada da Afrika ta Kudu da maki 8.7, Angola mai maki 8.3 sai Guinea da maki 7.8 a hasashen zama zakarun AFCON da ke gudana.

Majalisar tarayya ta fara tuhumar hukumar kwastam

A wani labarin kuma, majalisar tarayya ta fara titsiye hukumar hana fasa kwauri ta kasa, saboda gaza gabatar da bayanan kudinta na shekaru uku.

Majalisar na zargin cewa hukumar kwastam na boye wasu bayanai da suka shafi shige da ficen kudinta na shekarar 2016, 2017 da 2018.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.