Akwai Matsala: CAF Ta Zabi Babban Dan Wasan Najeriya Domin Yi Masa Gwajin Kwaya

Akwai Matsala: CAF Ta Zabi Babban Dan Wasan Najeriya Domin Yi Masa Gwajin Kwaya

  • CAF tana so ta san irin ƙarfin da ɗan wasan ƙwallon ƙafa na Najeriya Victor Osimhen, yake da shi
  • Wannan na zuwa ne bayan ƙwararren dan wasan ƙwallon ƙafan na Napoli, ya yi rawar gani a wasan Najeriya da Kamaru, wanda aka gudanar a ranar Asabar, 27 ga watan Janairu a Ivory Coast
  • Kwallon da Osimhen ya yi a karawar da ƙungiyar Indomitable Lions ta Kamaru da Super Eagles wacce Lookman ya zura ƙwallaye biyu, ya bar CAF cikin mamaki

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Hukumar ƙwallon ƙafa ta nahiyar Afirika (CAF) ta zaɓi ɗan wasan Najeriya, Victor Osimhen domin yi masa gwajin ƙwaya.

Gwajin na zuwa ne bayan fafatawar da Najeriya ta yi da Kamaru a wasan zagaye na 16 na gasar cin kofin AFCON 2023 a ranar Asabar, cewar rahoton Vanguard.

Kara karanta wannan

Daga karshe an bayyana dalilin da ya sanya ake kashe-kashe a Plateau

CAF za ta yi wa Osimhen gwajin kwaya
CAF za ta binciki lafiyar Victor Osimhen Hoto: Victor Osimhen
Asali: Facebook

Osimhen ne ya jagoranci Super Eagles a wasan da suka doke Kamaru da ci 2-0, inda ya riƙa neman ƙwallo a koda yaushe.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Meyasa CAF za ta yi wa Osimhen gwajin ƙwaya?

A ɗaya daga cikin irin waɗannan lokuta, Osimhen ya ƙwace ƙwallo daga hannun wani ɗan wasan baya na Kamaru, sannan ya tura wa Ademola Lookman wanda ya zura ƙwallon farko a ragar Kamaru.

Ya riƙa bin kowace ƙwallo kuma ya ci gaba da zama barazana ga tsaron Kamaru a tsawon lokacin da ya shafe a filin wasa.

Rashin gajiyar da ya nuna ya ja hankalin CAF, lamarin da ya sa aka zaɓo shi don yi masa gwaji.

Yawancin lokaci, ana zaɓar ƴan wasa ta hanyar yin ƙuri'a ga duk ƴan wasan da ke cikin tawagar ta ranar wasa.

Sai dai, ana iya ɗaukar ɗan wasa shi kaɗai idan an lura da wani sabon hali a tattare da shi.

Kara karanta wannan

Jega ya bayyana abu 1 da ya kamata a bincika kan zaben 2023

Kwankwaso Ya Taya Super Eagles Murna

A wani labarin kuma, kun ji cewa Rabiu Musa Kwankwaso ya taya ƙungiyar kwallon kafa ta Najeriya (Super Eagles) murnar zuwa zagaye na gaba a gasar cin kofin Nahiyar Afirka (AFCON2023).

Jigon na jam'iyyar NNPP ya ce ƙoƙarin da ƙungiyar Super Eagles ta yi na zuwa zagaye na gaba abin a yaba ne matuka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng