AFCON: Kwankwaso Ya Taya Tawagar Najeriya Nasarar Hayewa Mataki Na Gaba
- Rabiu Kwankwaso, jagoran jam'iyyar NNPP, ya taya kungiyar kwallon kafa ta Najeriya (Super Eagles) murnar lallasa kasar Guinea-Bissau
- Wannan nasarar da Super Eagles suka samu akan Guinea-Bissau ya ba su damar zuwa wasannin zagaye na 16 a gasar AFCON2023
- Kwankwaso ya karfafawa kungiyar guiwa tare da fatan za su ci gaba da samun nasara a wasannin su na gaba don lashe gasar kofin
Sani Hamza, kwararren edita ne a fanni n nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Jigon jam'iyyar NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso ya taya kungiyar kwallon kafa ta Najeriya (Super Eagles) murnar zuwa zagaye na gaba a gasar cin kofin Nahiyar Afirka (AFCON2023).
Kwankwaso ya ce kokarin da kungiyar Super Eagles ta yi na zuwa zagaye na gaba abin a yaba ne matuka.
Yadda tawagar Najeriya ta fafata zuwa mataki na gaba
A ranar Litinin, Super Eagles ta lallasa kungiyar kwallon kafa Guinea-Bissau da ci daya mai ban haushi, a wasan karshe na rukunin A wanda ya ba ta damar zuwa wasan zagaye na 16.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kungiyar wacce ke karkashin mai horo Jose Peseiro ta kara da Guinea-Bissau ne bayan fafatawa da kasar Ivory Coast wacce ita ma ta lallasa ta da ci daya mai ban haushi, rahoton Channels TV.
Duk da cewa sun sha matsin lamba a zagayen wasan na farko, sun dawo da karfinsu bayan zuwa hutu, inda dan wasan Guinea-Bissau ya zura kwallo a gidansu a kokari cire ta.
Sakon da Kwankwaso ya aika wa Super Eagles
A halin yanzu dai, Super Eagles za su ci gaba da zama a birnin Abidjan domin karawa ranar Asabar da kungiyar da za ta ci wasan rukunin C, tsakanin Senegal, Guinea ko Kamaru.
Rabiu Kwankwaso sakon taya murnar da ya aika wa Super Eagles a shafinsa na Twitter ya ce:
"Kun cancanci yabo na tsallakawa zuwa zagaye na gaba. Ku kara kokari don samun nasara a wasannin ku na gaba."
Karanta sakon a nan kasa:
Karatu da haddar Al-Kur'ani na gyara kwakwalwa - Gwamna AbdulRazaq
Gwamnan jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq ya ba al'ummar Musulmi musamman matasa shawarar mayar da hankali wajen karatu da haddar Al-Kur'ani mai girma.
A cewar Gwamna AbdulRazaq, haddar littafin mai tsarki na gyarawa tare da saita kwakwalwar mai karanta shi.
Asali: Legit.ng