Manyan Dalilai 6 da Ya Sanya Roma Korar Mourinho Daga Rike Ragamar Kungiyar
- A yau Talata 16 ga watan Janairu ce aka sallami kocin kungiyar kwallon kafa ta Roma, Jose Mourinho
- Mourinho ya fara aiki ne a matsayin kocin kungiyar a watan Mayun 2021 kasa da wata daya bayan korar shi a Tottenham Hotspur
- Legit Hausa ta jero muku manyan dalilan da ya sanya Roma raba gari da fitaccen kocin a duniya a yau Talata
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Roma, Italiya - Kungiyar kwallon kafa ta Roma ta sallami kocinta, Jose Mourinho saboda rashin tabuka wani abu.
Kungiyar a yanzu haka tana mataki na tara a teburin gasar kasar Italiya da aka fi sani da 'Seria A'.
Yaushe aka dauki hayar Mourinho a Roma?
Mourinho dan kasar Portugal Mai shekaru 60 a duniya ya taimaka wa Roma lashe gasar Europa Conference, cewar ESPN.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kungiyar ta nada Mourinho a watan Mayun 2021 kasa da wata daya bayan an sallame shi a kungiyar Tottenham Hotspur.
Legit Hausa ta jero muku manyan dalilan da ya sa aka sallami Mourinho daga mukaminsa:
1. A makon da ya gabata, an cire Roma daga gasar Coppa Italia, kamar yadda Sky Sport ta tattaro.
Abokiyar hamayyarsu da suke cikin gari daya Lazio ita ta yi nasarar cire Roma daga gasar.
2. Rashin tabuka abin a zo a gani a wannan kakar wasan na daga cikin dalilan korar Mourinho.
3. Wani babban dalilin korar Mourinho kuma shi ne kungiyar ta na lanjane a mataki na tara a teburin gasar.
4. Kungiyar Roma ta na mataki na tara a teburin wanda suke neman maki biyar don haurowa zuwa matakin rukunin gasar zakarun Turai.
5. Roma ta yi rashin nasara a gasar Serie A da ci kwallo 3 da 1 a hannun Milan a ranar Lahadi 14 ga watan Janairu.
Wannan shi ne rashin nasara karo na uku cikin wasanni biyar da suka yi, cewar The Nation.
6. Kwanritagin da Mourinho ya sanya wa hannu zai kare a watan Yunin wannan shekara da muke ciki.
Kano Pillars ta nemi gafara ga hukumar NFFL
A wani labarin, Kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars ta nemi afuwa kan cin tarar ta da aka yi a gasar Firimiya ta Najeriya.
Kungiyar ta ce wannan mataki ya yi tsauri inda ta ke neman sassauci ganin yadda magoya bayanta ke kokarin bin dokar gasar.
Asali: Legit.ng