Kano Pillars Ta Durkusa Gaban Hukumar NFFL, Ta Nemi Taimako Kan Dalili 1, Bayanai Sun Fito

Kano Pillars Ta Durkusa Gaban Hukumar NFFL, Ta Nemi Taimako Kan Dalili 1, Bayanai Sun Fito

  • Kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars ta nemi gafara a gaban kwamitin ladabtarwa ta hukumar NFFL
  • Pillars ta yi wannan rokon ne bayan cin tarar kungiyar da aka yi har naira miliyan 12 saboda tarzoma da magoya bayanta suka jawo
  • Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da sakataren kungiyar, Sani Ibrahim ya fitar a jiya Talata 9 ga watan Janairu

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Hukumar Kungiyar Kwallon Kafa ta Kano Pillars ta nemi alfarma a wurin Kwamitin ladabtarwa ta Hukumar NFFL.

Kano Pillars ta yi wannan rokon ne bayan an ci tarar kungiyar har naira miliyan 12 saboda ta da tarzoma a filin wasa a Kano.

Kara karanta wannan

Kano: Kotu ta dauki mataki kan dan daba da ya kashe limami, ta kuma hada da mahaifinsa

Kano Pillars ta roki sassauci daga hukumar NFFL a Najeriya
Kano Pillars ta roki gafara kan abin da ya faru a Kano. Hoto: Kano Pillars.
Asali: Facebook

Mene dalilin cin tarar Kano Pillars?

Hukumar kwallon kafa na Najeriya, NFF ta yi binkice karkashin jagorancin kwamitin ladabtarwa inda aka samu Kano Pillars da laifuka da dama da suka saba ka'idojin gasar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hakan ya biyo bayan tada hankula da jifan alkalan wasa a cikin filin wasan Sani Abacha yayin wasa da Plateau United, Premium Times ta tattaro.

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da sakataren kungiyar, Sani Ibrahim ya fitar a jiya Talata 9 ga watan Janairu.

Meye martanin Kano Pillars?

Sanarwar ta ce:

"Mun yi Allah wadai da abin da ya faru amma muna rokon kwamitin ya rinka kai zuciya nesa kan irin wannan matsalar a matsayinsa na wanda ba shi da son kai a tsakani.
"Tabbas dan Adam tara ya ke bai cika goma kuma bai fi karfin kuskure ba amma a bi hanyar da ta dace don ganin an yi hukunci cikin tausaya wa.

Kara karanta wannan

Shehu Sani ya yi martani yayin da Tinubu ya dakatar da Betta Edu, ya yi shagube ga Buhari

"Har ila yau, magoya bayan kungiyar Kano Pillars suna iya kokarinsu wurin ganin sun bi dokokin wasanni amma abin mamaki wasu na kokarin bata lamarin da tashin hankali."

Ibrahim ya kara da cewa tabbas matsalar ta shafi kungiyar musamman a kokarin da suke yi a wannan gasa, cewar Daily Trust.

Har ila yau, kungiyar ta ce za ta yi duk mai yiyuwa don ganawa da shugabannin magoya bayanta don samun yadda za a shawo kan lamarin.

Ta kuma roki gafara kan lamarin da ya faru inda ta ce wasu tsiraru ne suka shiga cikinsu don ganin sun zubar musu da kima.

Kofarmata ya rasu a Kano

A wani labarin, tsohon dan kwallon kafar Kano Pillars, Bello Kofarmata ya Riga mu gidan gaskiya.

Kofarmata ya rasu ne ya na da shekaru 34 bayan ya yi fama da jinya a Unguwar Kofarmata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.