Auwalu Musa Zakirai: Tsohon Sakataren Kano Pillars Da Ya Fi Kowa Daɗe Wa Kan Muƙamin Ya Rasu

Auwalu Musa Zakirai: Tsohon Sakataren Kano Pillars Da Ya Fi Kowa Daɗe Wa Kan Muƙamin Ya Rasu

  • Tsohon sakataren kungiyar wasan kwallon kafa ta Kano Pillar kuma sakataren kungiyar mafi dadewa, Alhaji Auwalu Musa Zakirai ya mutu jiya yana da shekaru 70 da haihuwa
  • Jami’in watsa labaran kungiyar Kano Pillars FC, Alhaji Idris Rilwanu Malikawa ya sanar da rasuwar ta wata takarda da safen nan inda ya ce ya yi gajeriyar jinya
  • A takardar, an samu bayanai akan yadda ya mutu ya bar matarsa da yara 15 da kuma jikoki da dama wanda mutuwarsa ta girgiza kungiyar wasan kwallon kafan Jihar Kano da kuma ta Najeriya gaba daya

Jihar Kano - Allah ya yi wa Tsohon Sakataren Kungiyar wasan kwallon kafa ta Kano Pillars, Alhaji Auwalu Musa Zakirai rasuwa yana da shekaru 70 da haihuwa a jiya, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Na cancanci gaje kujerar Buhari: Inji Amaechi ga jama'ar Katsina yayin wata ziyara

An samu bayanai akan yadda Zakirai ya kasance sakataren kungiyar mafi dadewa, kuma ya rasu ne bayan gajeriyar jinyar da ya yi a Asibitin Muhammad Abdullahi Wase da ke Kano.

Tsohon Sakataren Kano Pillars Da Ya Fi Kowa Daɗe Wa Kan Muƙamin Ya Rasu
Auwalu Musa Zakirai: Tsohon Sakataren Kano Pillars Da Ya Fi Kowa Daɗe Wa Kan Muƙamin Ya Rasu. Hoto: Daily Trust.
Asali: Twitter

Jami’in watsa labaran kungiyar Kano Pillars FC, Alhaji Idris Rilwanu Malikawa ya bayyana mutuwar inda ya ce ya mutu ya bar matarsa daya, yaransa 15 da kuma jikoki da dama.

Mutuwarsa ta girgiza jama’a da dama

Marigayi Auwalu Zakirai a lokacin da ya ke da rai ya jajirce wurin tabbatar da ci gaban kwallon kafa a Jihar Kano da kasa baki daya.

Mutuwar ta shi ta girgiza gabadaya kungiyar wasan kwallon kafar Jihar Kano da ta kasa baki daya kamar yadda Nigerian Sketch ta ruwaito.

Yayin mika ta’aziyya ga iyalan mamacin, shugaban kungiyar wasan kwallon kafa ta Kano Pillars, Alhaji Surajo Shuaibu Yahaya ‘Jambul’ ya kwatanta marigayi Zakirai a matsayin mutum mai kamun kai, mai gaskiya da kuma dage wa jiharsa don ba za a taba mantawa da shi ba a tarihin kungiyar wasan kwallon kafa ta Kano Pillar da ta kasa baki daya ba.

Kara karanta wannan

2023: Amaechi ya fara neman shawarwari, ya ziyarci sarakunan Daura, Kano da Bichi

Shugaban kungiyar na Jihar Kano ya ci gaba da yi masa fatan samun rahama da yafiyar Allah akan dukkanin kura-kuransa kuma ya yi masa fatan samun Jannatul Firdausi.

Matar Shahararren Tsohon Gwamnan Najeriya Ta Rasu a Asibiti a Amurka

A wani labarin, Njideka Ezeife, matar tsohon gwamnan jihar Anambra wanda kuma dattijo ne a kasa, Chief Chukwuemeka Ezeife ta riga mu gidan gaskiya.

Njieka ta rasu ne bayan fama da gajeruwar rashin lafiya a wani asibiti da ke Amurka kamar yadda kungiyar dattawan Igbo ta sanar ta bakin sakatarenta Farfasa Charles Nwekeaku, The Sun ta ruwaito.

Nwekeaku ya ce ana sa ran tsohuwar matar gwamnan za ta dawo Najeriya ne a ranar Litinin, 13 ga watan Disamban 2021 amma kwatsam ta fara rashin lafiya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel