Shugaba Tinubu Ya Amince da Biyan N12bn Na Bashin Yan Wasan Super Eagles da Sauransu
- Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da biyan bashin N12bn na tawagar ƴan wasan Supers Eagles da suka biyo
- Kuɗaɗen sun haɗa da basussukan watanni 15 da kocin manyan tawagar ƙungiyoyin wasanni daban-daban suke bi
- Tawagar ƴan wasan na Super Eagles da na mata da ƴan ƙasa da shekara 20 za su samu kuɗaɗen alawus ɗinsu da aka yi musu alƙawari
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya amince da biyan Naira biliyan 12 domin biyan bashin ƴan wasan Super Eagles da sauran ƙungiyoyin Najeriya na wasanni daban-daban.
A cewar wata sanarwa da aka fitar a shafin X na cibiyar yaɗa labarai ta shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, biyan kudin ya haɗa da biyan albashin manyan kocin ƙungiyar na ƙasa na tsawon watanni 15.
Kuɗaɗen sun kuma haɗa da biyan alawus-alawus da alƙawuran da aka yi wa manyan ƙungiyoyin da suka haɗa da na mata da na ƴan ƙasa da shekara 20.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Su wanene za su amfana da kuɗin?
Sanarwar na cewa:
"Shugaba Tinubu ya amince da biyan N12bn na bashin ƙungiyoyin wasanni daban-daban na Najeriya, wanda ya haɗa da Super Eagles da sauransu.
"Biyan ya haɗa da biyan albashin manyan kocin ƙungiyoyin na tsawon watanni 15, da biyan alawus-alawus da kuma alƙawuran da aka yi wa manyan ƙungiyoyin na ƙasa da suka haɗa da mata da kuma ƴan ƙasa da shekara 20.
"Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da Super Eagles ta Najeriya ke shirin shiga gasar cin kofin nahiyar Afirika da za a fara a ƙarshen wannan wata."
Minista Ya Faɗi Abin da Ke Hana Tinubu Barci
A wani labarin kuma, kun ji cewa ƙaramin ministan lafiya, Tunji Alausa ya ce shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya damu da yadda wasu abubuwa su ke faruwa a Najeriya.
Dakta Tunji Alausa ya ce irin tashin farashin magunguna da ƙarancin muhimman magunguna su na ba shugaban ƙasan ciwon kai.
Asali: Legit.ng