Jamus: Jerin Manyan Filayen Wasa 10 da Za Su Karbi Bakuncin Buga Gasar EURO 2024

Jamus: Jerin Manyan Filayen Wasa 10 da Za Su Karbi Bakuncin Buga Gasar EURO 2024

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Kasar Jamus - Manyan filayen wasa 10 aka zaba a fadin kasar Jamus don karbar bakuncin gasar EURO 2024.

Daga filayen da aka buga wasan karshe na gasar Champions League, Kofin Duniya, zuwa filayen da ake buga manyan wasanni a kasar.

Ga bayani kan filayen guda 10, wanda jaridar Vanguard ta tattaro.

Olympiastadion Berlin
Filin wasa na Olympiastadion Berlin Hoto: Eurofoot
Asali: Twitter
  • Berlin

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Asalin suna: Olympiastadion Berlin

Berlin za ta dauki mutum dubu 70 a wasannin gasar Euro, sababin mutum dubu 74 da ta saba dauka.

Babbar kungiyar da ke taka leda a yankin da filin wasan ya ke ita ce kungiyar Hertha Berlin (a rukuni na biyu)

Kara karanta wannan

Nasara daga Allah: Sojoji sun kakkabe 'yan ta'adda 180 tare da kubutar da mutum 234

Kaddamarwa: A shekarar 1936 aka kaddamar da filin wasan, sannan aka sabunta shi a 2,000 da 2004.

A baya dai an gudanar da gasar Olympics ta Berlin a filin a 1936; gasar kofin duniya na 2006, da ya hada da wasan karshe; gasar motsa jiki ta duniya a 2006, da ya hada da wasan karshe; gasar Champions League ta 2015.

Euro 2024: Za a buga wasanni uku ba kungiyoyi, wasa na 16, wasa ba biyu da na karshe da kuma wasan karshe.

Fussball Arena Muenchen
Filin wasa na Fussball Arena Muenchen Hoto: @FCBayern
Asali: Twitter
  • Munich

Asalin suna: Fussball Arena Muenchen

Munich zai dauki mutane dubu 67 a gasar Euro sabanin mutum dubu 75 da ya saba dauki.

Kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munich ita ce babbar kungiyar da ke yankin Munich.

An kaddamar da filin a shekarar 2005.

Wasannin da aka buga a filin a baya: Kofin duniya na 2006, da ya hada da wasan farko; wasan karshe na gasar Champions League a 2012; gasar Euro 2020; wasan karshe na Champions League 2025 (mai zuwa).

Kara karanta wannan

An ga tashin hankali yayin da 'yan bindiga su ka sace shahararren malamin addini da wani mutum 1

Wasannin da za a buga a gasar Euro 2024: Wasanni na rukunoni uku, da suka hada da wasan farko; wasa na 16 da kuma wasa na kusa da na karshe.

Dortmund Stadium
Filin wasa na Westfalenstadion Hoto: BVB
Asali: Twitter
  • Dortmund

Asalin suna: Westfalenstadion

Dortmund za ta dauki mutum dubu 66 a gasar Euro sababin mutum dubu 81 da ta saba dauka.

Kungiyar Borussia Dortmund ce ke taka leda a yankin Dortmund.

An kaddamar da filin a shekarar 1974, sannan aka sabunta a 1992, 1999, 2003 da 2006.

Wasannin da aka buga a baya: Kofin duniya 1974; wasan karshe na kofin UEFA (C3) 2001; kofin duniya na 2006.

Wasannin da za a buga a gasar Euro 2024: wasannin rukunoni hudu, wasa na 16 da kuma wasa na kusa da na karshe.

Neckarstadion
Filin wasa na Neckarstadion Hoto: VfB
Asali: Twitter
  • Stuttgart

Asalin suna: Neckarstadion

Stuttgart za ta dauki mutum dubu 54 sabanin mutum dubu 60.5 da ta saba dauka.

Kungiyar VfB Stuttgart ce ke taka leda a yankin Stuttgart.

Kara karanta wannan

Jami'an tsaro sun halaka dan bindiga, sun ceto malamin addini da wasu mutum 2 a jihar arewa

An kaddamar da filin a watan Yuli 1933, an sabunta a 1951, 1993, 2004, 2011 da 2024.

Wasannin da aka buga a filin a baya: Wasan karshe na Champions League 1959; kofin duniya 1974; wasan karshe na Champions League 1988; gasar Euro 1988; gasar motsa jiki ta duniya a 1993; kofin duniya na 2006.

Wasannin da za a buga a gasar Euro 2024: Wasannin rukunoni hudu da wasa na biyun karshe.

Volksparkstadion
Filin wasa na Volksparkstadion Hoto: HSV
Asali: Twitter
  • Hamburg

Asalin suna: Volksparkstadion

Filin Hamburg zai dauki mutum dubu 50 a gasar Euro sabanin mutum dubu 55 da ya saba dauka.

Kungiyar Hamburg SV (rukuni na biyu) ke taka leda a yankin Hamburg.

An kaddamar da filin a watan Yuli 1953, an yi masa gyara a 1998-2000, 2006, 2010 da 2024.

A baya: An buga gasar Kofin Duniya 1974; Euro 1988; Kofin Duniya 2006; Wasan karshe na gasar Europa 2010.

A yanzu: Za a buga wasannin rukunoni hudu na gasar Euro 2024 da kuma wasa na biyu na kusa da na karshe.

Kara karanta wannan

Murna yayin da a karshe FG ta bayyana ranar biyan basukan masu cin gajiyar N-Power, ta fadi dalilai

Duesseldorfer Arena
Filin wasa na Duesseldorfer Arena Hoto: f95
Asali: Twitter
  • Duesseldorf

Asalin suna: Duesseldorfer Arena

Duesseldorf za ta dauki mutum dubu 47 a wasan Euro sabanin mutum dubu 50 da ta saba dauka.

Fortuna Duesseldorf (rukuni na biyu) ita ce babbar kungiyar da ke fafatawa a yankin Duesseldorf.

An kaddamar da filin wasan a watan Janairun 2005.

Wasannin da aka buga a baya: Wasan karfe na takwas na gasar Eurofa 2020; bude gasar wasan kwallon hannu na maza a Euro 2024 (mai zuwa)

Wasan da za a buga a gasar Euro 2024: Wasannin rukunoni uku, wasa na daya na 16, wasa na kusa da na kusa da na karshe.

Muengersdorfer Stadion
Filin wasa na Muengersdorfer Stadion Hoto: Fccoeln
Asali: Twitter
  • Cologne

Asalin suna: Muengersdorfer Stadion

Filin Cologne zai dauki mutum dubu 47 a gasar Euro 2024 sabanin mutum dubu 50 da ya saba dauka.

FC Cologne ita ce babbar kungiyar da ke taka leda a yankin Cologne.

An kaddamar da filin a watan Satumba 1923, an yi gyara a 1975 da 2004.

Kara karanta wannan

Yan Boko Haram sun datse kawunnan mutane 11 masu sana’ar itace a Borno

A shekarun baya: An buga gasar Euro 1988 a filin; kofin Confederation 2005; kofin duniya 2006; wasan karshe na 8 da kuma wasan karshe na gasar Europa 2020.

Wasannin da za a buga a gasar Euro 2024: Wasannin rukunoni hudu da wasa na daya na 16.

Waldstadion
Filin wasa na Waldstadion Hoto: Eintracht
Asali: Twitter
  • Frankfurt

Asalin suna: Waldstadion

Filin Frankfurt zai dauki mutum dubu 48 a gasar Euro sabanin mutum dubu 55 da ya saba dauka.

Kungiyar kwallon kafa ta Eintracht Frankfurt ne ke taka leda a yankin Frankfurt.

An kaddamar da filin a watan Mayun 1925, an fadada shi a 1937 da 1953, sannan an yi masa gyara a 1974 da 2005.

A baya: An buga wasan Kofin Duniya na 1974, ciki har da wasan farko na bude gasar; Euro 1988; Kofin Confederation 2005; Kofin Duniya 2006; wasan karshe na gasar kofin mata na duniya 2011.

A gasar Euro 2024: Za a buga wasannin rukunoni hudu da wasa daya na 16.

Kara karanta wannan

Daga musayar magana: Ango ya kashe amaryarsa da surukarsa a ranar aurensu

Zentralstadion
Filin wasa na Zentralstadion Hoto: RB Leipzig
Asali: Twitter
  • Leipzig

Asalin suna: Zentralstadion

Filin Leipzig ya saba daukar mutum 47,069 amma zai dauki mutum dubu 42 a gasar Euro.

Kungiyar kwallon kafa ta RB Leipzig ce babbar kungiya a yankin Leipzig.

An kaddamar da filin a watan Nuwamba 2004, an kuma fadada shi a shekarar 2021.

A baya: An buga wasan Kofin Confederation na 2005; Kofin Duniya na 2006.

A gasar Euro 2024: Za a buga wasannin rukunoni uku da wasa na daya na 16.

Arena AufSchalke
Filin wasa na Arena AufSchalke Hoto:FC Schalke 04
Asali: Twitter
  • Gelsenkirchen

Asalin suba: Arena AufSchalke

A baya filin Gelsenkirchen na daukar mutum dubu 54,740 amma a gasar Euro zai dauki mutum dubu 50.

An kaddamar da shi a watan Agusta 2001, an yi masa babban gyara a 2005.

Kungiyar kwallon kafa ta Schalke 04 (rukuni na biyu) ita ce ta ke taka leda a yankin Gelsenkirchen.

A baya: An buga wasan karshe na gasar Champions 2004; Kofin Duniya na 2006; wasan farko na kofin duniya na wasan kankara 2010; wasan takwas na karshe a gasar Europa 2020.

A gasar Euro 2024: Za a buga wasannin rukunoni uku da wasa daya na wasanni 16 na karshe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.