Mai Tsaron Gidan Manchester, Onana Ya Bayyana Cewa Maye Gurbin De Gea Babban Kalubale Ne

Mai Tsaron Gidan Manchester, Onana Ya Bayyana Cewa Maye Gurbin De Gea Babban Kalubale Ne

  • Mai tsaron gida na kungiyar Manchester United ya bayyana kalubalen da ya ke fuskanta kan maye gurbin De Gea
  • Onana ya ce tabbas maye gurbin De Gea a Manchester ya fi komai tashin hankali a wurinshi
  • Ya bayyana haka ne yayin da kungiyarsa ke shirin karawa da Bayern Munich a gasar zakarun Turai a daren yau

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Mancheter, Ingila - Andre Onana, mai tsaron gidan kungiyar kwallon kafa ta Manchester United ya ce tabbas maye gurbin De Gea ba abu ne mai sauki ba.

Onana ya bayyana haka ne a yayin da kungiyarsu ke shirin karawa da kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munich a gasar zakarun Turai da za a fafata a yau.

Onana ya bayyana kalubalen maye gurbin De Gea
Mai Tsaron Gidan Manchester, Onana Ya Yi Martani Kan Maye Gurbin De Gea. Hoto: Andre Onana (Facebook).
Asali: Facebook

Meye Onana ke cewa ka De Gea?

Dan kwallon kasar Kamarun ya ce ya na da kwarin gwiwar cewa kungiyarsu za ta bai wa Bayern kashi a daren yau Laraba 20 ga watan Satumba.

Kara karanta wannan

Hukuncin Zabe: Hankula Sun Tashi Yayin Da Aka Rufe Shaguna A Kano, Bayanai Sun Fito

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Tribal Football ta tattaro Onana na cewa:

"Ina murnan kasancewa ta a nan, amma kamar yadda na saba fada maye gurbin De Gea ba abu ba ne mai sauki, zan ci gaba da kokari sosai.
"Ina matukar son wasan kwallo kuma ina bukatar goyon baya sosai daga masu tsaron gida a wannan kungiya.
"Kasancewa a wannan babbar kungiyar kwallon kafa abin alfahari ne a wuri na da kuma duk wani dan wasa."

Yaushe Onana ya zo Manchester?

Onana ya rattaba hannu a kungiyar Manchester United har na tsawon shekaru biyar zuwa 2028 kan kudi Yuro miliyan 47.2.

An zura masa kwallaye har 10 a wasanni biyar kacal da aka buga a gasar Firimiya ta Ingila, Caughtoffside ta tattaro.

Ya kara da cewa a farko kakar wannan shekarar ba su samu abin da su ke tsammani ba, inda ya ce ya na da kwarin gwiwar cewa za su shawo kan matsalar.

Kara karanta wannan

Yadda Likita Ya Yanke Jiki Ya Mutu Bayan Ya Shafe Tsawon Awanni 72 Yana Aiki a Asibitin LUTH

A cewarsa:

"Farkon wannan kakar ba mu samu abin da mu ka yi tsammani ba, amma ina da kwarin gwiwar cewa komai zai daidaita."

Onana zai fara buga gasar zakarun Turai ta farko a Manchester a daren yau tun bayan barinshi kungiyar Inter Milan a kakar bara.

Manchester za ta kara da kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munich a kasar Jamus.

Magoyan bayan Juventus sun nuna kiyayya ga Lukaku

A wani labarin, magoyan bayan kungiyar kwallon kafa ta Juventus sun nuna tsan-tsar kiyayya ga Romelu Lukaku.

Kungiyar na shirin siyan dan wasan inda magoya bayan su ka nuna ba sa bukata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.