'Yar Kwallon Najeriya Asisat Oshoala Ta Ce Mahaifinta Ba Zai Ji Dadin Cire Rigar Da Ta Yi Don Murna Ba
- Zaƙaƙurar 'yar ƙwallon mata ta Najeriya Asisat Oshoala ta bayyana yadda mahaifinta zai ji saboda cire rigar da ta yi
- Ta ce mahaifin na ta ba zai ji daɗi ba ganin yadda ta tuɓe rigarta a lokacin da ta zura ƙwallo ta uku a wasansu da Australia
- Mutane da dama sun yi martani kan hoton na Asisat da kuma rubutun da ta wallafa a shafinta na Instagram
Yar ƙwallon mata ta Najeriya Asisat Oshoala ta bayyana cewa mahaifinta ba zai ji dadi ba dangane da salon murnar da ta yi lokacin da suka ci Australia 3 - 2.
Ta bayyana hakan ne a wani rubutu da ta wallafa a shafinta na Instagram ranar juma'a.
Menene Asisat Oshoala ta yi? Ƙarin bayani
An dai sanyo Asisat ne a zagaye na biyu na wasan ƙwallo da ake bugawa tsakanin mata na Super Falcons da ke wakiltar Najeriya, da abokan karawarsu na Australia.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
A lokacin da 'yar ƙwallon ta Najeriya Asisat Oshoala ta shigo, kowane ɓangare na ƙasashen biyu ya zura ƙwallaye biyu a raga kamar yadda Vanguard ta ruwaito.
An ci gaba da buga wasa inda ana cikin hakan ne Asisat ta yi nasarar zura ƙwallo ta uku ga kulob ɗin Super Falcons na 'yan Najeriya, wanda hakan ya ba su nasara kan abokan karawar na su.
Tsananin murna ce ta sanya Asisat tuɓe rigarta ta ƙwallo, wanda hotonta da aka ɗauka a lokacin ya karaɗe kafafen sada zumunta.
Hotunan na ta sun kuma janyo kace nace tsakanin masu amfani da kafafen sada zumunta.
Masu amfani da kafafen sada zumunta sun yi martani kan jawabin na Asisat Oshoala
Asisat ta wallafa a shafinta na Instagram cewa, ta san lallai mahaifinta ba zai ji daɗin hanyar da ta bi wajen nuna farin cikinta a lokacin da ta zura ƙwallo ta uku ba.
Bidiyon Davido: Hadimin Mawaƙin Ya Goge Rubutun Neman Afuwa Da Ya Yi Yayin Da Ya Ƙi Bai Wa Musulmai Haƙuri
Mabiyan fitacciyar yar ƙwallon a shafinta na Instagram, sun yi martani kan rubutun da ta yi inda wasu ke ganin babu komai tunda duk cikin murna ne.
Ga abinda wasu daga cikinsu ke cewa.
lolaomotayo_okoye ta ce:
“Za mu ba mahaifin naki haƙuri a madadin ki, muna alfahari da ke.”
officialyetundebakare ta ce:
“A madadin mu 'yan Najeriya, muna bai wa mahaifin naki haƙuri. Yi haƙuri Alhaji.”
segun_amusan1 ya ce:
“Ina taya ta murna. Wannan ya nuna irin gidan da ta fito. Sanin cewa mahaifinta ba zai ji daɗin cire rigar da ta yi ba don murna ga nuna cewa ta samu tarbiyya ta ƙwarai."
“Maganar da ta yi darasi ce ga duk wasu iyaye da ke goyon bayan shigar banza da 'ya'yansu ke yi da sunan kwalliya ko wayewa.”
“Na ƙaru da wani abu ɗaya dangane da rubutun nan na Oshoala, shi ne ka tarbiyyantar da yaronka ta yanda ko a bayan idanunka ya san abinda kake so da kuma wanda ba ka so.”
Wani matashi mai hannu ɗaya ya nuna ƙwarewa a wasan ƙwallon ƙafa
Legit.ng a baya ta kawo muku bidiyon wani matashi mai hannu ɗaya da yake wasan ƙwallo cikin ƙwarewa.
Bidiyon matashin a yayin da yake jujjuya ƙwallon ya yaɗu sosai a kafar sada zumunta ta TikTok.
Asali: Legit.ng