Mata Ta Koka Yayin Da Mijinta Ya Barta a Amurka Ya Dawo Afrika Ya Auri Wata

Mata Ta Koka Yayin Da Mijinta Ya Barta a Amurka Ya Dawo Afrika Ya Auri Wata

  • Wata mata da ke zaune a ƙasar Amurka, ta bayyana yadda mijinta ya ƙara aure ba tare da saninta ba
  • Matar mai suna Agnes Johnson, ta bayyana yadda mijin nata ya baro a Amurka ya dawo Afrika ba tare da sanar da ita ainihin abinda zai yi ba
  • Ta taya shi murna a shafinta na Facebook, tare da wallafa hotunansa da na amaryar tasa

Wata mata 'yar asalin ƙasar Liberia mai suna Agnes Johnson, ta bayyana yadda mijinta ya barota a ƙasar Amurka da suke zaune a tare, inda ya dawo Afrika domin ƙara aure.

Ta bayyana hakan ne a wani rubutu da ta wallafa a shafinta na Facebook, wanda Legit.ng ta ci karo da shi.

Mata ta taya mijinta murna bayan ƙara aure ba tare da saninta ba
Mata ta taya mijinta murnar auren da ya ƙara ba tare da saninta ba. Hoto: Agnes Johnson
Asali: Facebook

Ta taya mijin nata murnar angwancewa da ya yi

Kara karanta wannan

“Na Fi Mijina Samun Kudi”: Matar Aure Ta Ce Bata Bude Asusun Hadin Gwiwa Ba a Gidan Aurenta

Matar a cikin rubutun da ta wallafa a shafin nata, ta bayyana cewa mijinta mai suna Abu Sanoe ya barta a Amurka inda ya koma gida Afrika a kwanakin baya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ta ce ya yi aure yayin da yaje Afrika ba tare da ya faɗa ma ta ba, wanda ta ce ko ya yi tunanin ba za ta sani ba.

Sai dai Agnes ta taya mijin nata murna, tare da yi masa fatan alkhairi.

Sannan ta kuma miƙa godiyarta ga Ubangiji da ya bayyana hakan a gareta duk da mijin nata bai so ta sani ba.

Ga labarin kamar yadda ta wallafa a shafinta na Facebook:

Mutane sun yi martani kan rubutun matar da mijinta ya ƙara aure ba tare da sanar da ita ba

Mutane da dama sun shiga sashen sharhi na rubutun da matar ta wallafa domin tofa albarkacin bakunansu kana lamarin.

Kara karanta wannan

"Allah Ya Isa Ba Zan Taba Yafe Maka Ba": Fati Muhammad Ta Yi Martani Ga Mutumin Da Ya Yi Mata Kazafi a Soshiyal Midiya

Chinweike Omabe ya ce:

“Na miji zai iya auren mata biyu a nan Afrika.”

Oyizamie classic Kha'deejah ta ce:

“Wata ƙila kawai ya yi hoto da amaryar ne a matsayinsa na abokin ango.”

Kasuwa Snr ya ce:

“Ba wani mugun abu ba ne, na sake maimaitawa, ba wani mugun abu ba ne.”

Ma Ke Nnah ta ce:

“Zai zo ya ce miki ba shi ba ne, haɗawa kawai aka yi.”

Monet Roshie ta ce:

“Kin dai sanar da 'yan sanda ko? Ya kamata su jira shi a filin saukar jiragen sama idan ya dawo, ko kuma ya ci gaba da zama a ƙauyensu.”

Dan kasuwa ya nemi a raba aurensa da matarsa saboda dukan da take masa

Legit.ng a baya ta yi wani rahoto kan wani ɗan kasuwa mai suna Raphael Chima da ya maka matarsa gaban kuliya a Abuja.

Ya nemi a raba aurensu saboda dukan da ya ce tana lakaɗa masa sannan ba ta girmama iyayensa.

Kara karanta wannan

“Karin ‘Da 1 Kacal Na Nema”: Magidanci Ya Koka Yayin da Matarsa Ta Haifo Tagwaye, Ta Mika Masa Su a Bidiyo

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng