Kungiyar Al-Hilal Da Ke Saudiyya Za Ta Sayi Mbappe Akan Kudi Fiye Da €300m
- Tun bayan samun matsala da hukumomin kungiyar PSG, kungiyoyi da dama ke zawarcin Kylian Mbappe
- Mbappe ya samu matsala da kungiyar ne bayan ya ki amincewa ya tsawaita kwantiraginsa a kungiyar
- PSG ta cire sunansa a jerin 'yan wasan da za su tafi Gabas ta Tsakiya don buga wasannin share fagen kakar bana
Paris - Kungiyar kwallon kafa ta Al-Hilal da ke Saudiyya ta mika fiye da Yuro miliyan 300 don siyan shahararren dan kwallon kafa ta PSG, Kylian Mbappe, rahotanni sun ce PSG ta amince da tayin.
Mbappe dai na takun saka da kungiyarsa ta PSG bayan bayyana musu cewar ba zai tsawaita kwantiraginsa ba da zai kare a 2024.
Tushen matsalar da ta afku tsakanin Mbappe da PSG
Mbappe ya ki tsawaita kwantiraginsa, wanda akan ya fusata kungiyar inda suka cire sunansa a jerin 'yan kwallon da za su tafi Gabas ta Tsakiya don buga wasannin share fagen kakar bana, cewar gidan talabijin na Channels.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Daga bisani, kungiyar ta sa Mbappe a kasuwa inda ake rade-radin cewa zai koma Real Madrid da buga tambola, kamar yadda dan jarida, Fabrizio Romano ya tabbatar a shafinsa na Twitter.
Bayan Al-Hilal akwai kungiyoyi da ke zawarcin Mbappe kamar su Arsenal da Barcelona da Manchester United da ke son dauko dan wasan.
Sai dai har yanzu ba a ji komai daga dan wasan ko kuma wakilansa ba akan wannan ciniki da ake shirin kullawa.
Garabasar da Mbappe zai kwashe a Al-Hilal ta Saudiyya
Al-Hilal na son dauko Mbappe bayan wasu 'yan wasa daga gasar Premier sun koma buga tambola a kungiyar da ke da arziki.
Mbappe zai samu £893,000 a ko wane mako, yayin da shekara daya zai kwashi makudan kudade har £80m.
Har ila yau, dan wasan zai samu alawus da ya kai £100m, Soccernet.ng ta tattaro.
Tun bayan sauya sheka zuwa kungiyar kwallon kafa ta Al-Nassr da Christiano Ronaldo ya yi, 'yan wasa da dama ke kokarin komawa Saudiyya don kwashe kudade masu tsoka.
Da Alamu Messi Zai Koma Wasa A Saudi A Cinikin Da Zai Girgiza Duniyar Kwallo
A wani labarin, akwai alamu Lionel Messi zai iya komawa kasar Saudiyya da buga kwallon kafa.
Rahotanni sun tabbatar da cewa dan wasan gaban na kasar Argentina zai raba gari da PSG, bayan alakarsu ta tabarbare a 'yan kwanakin nan.
Kungiyar Al-Hilal ta yi wa Messi tayin Yuro miliyan 522 duk da cewa babu tabbas hakan zai kasance.
Asali: Legit.ng