Tsansan Kyawu Na Wasu Jami’an Soji Mata Biyu Ya Dauki Hankali, Bidiyonsu Ya Yadu

Tsansan Kyawu Na Wasu Jami’an Soji Mata Biyu Ya Dauki Hankali, Bidiyonsu Ya Yadu

  • Wasu dakarun sojoji mata biyu masu ji da tsantsar kyawu sun shahara a soshiyal midiya sannan sun haddasa cece-kuce a TikTok
  • Bidiyon da ya yadu ya hasko sojojin biyu da suka gaji da haduwa don kyau yayin da suke rera wakar wani mawaki dan Najeriya, Davido
  • Bidiyon ya tara 'likes' kimanin 27.7k, martani fiye da 600 da kuma mutum fiye da 417k da suka kalla

Masu amfani da manhajar TikTok sun mato a kan wani bidiyo na wasu jami'an sojoji mata biyu da suka gaji da haduwa don kyau.

Shafin @jessybrass ne ya wallafa bidiyon dakarun da ke aiki a rundunar sojojin Amurka kuma tuni ya yadu.

Dakarun sojoji mata
Tsansan Kyawu Na Wasu Jami’an Soji Mata Biyu Ya Dauki Hankali, Bidiyonsu Ya Yadu Hoto:TikTok/@jessybrass.
Asali: UGC

A cikin dan gajeren bidiyon an hasko dakarun sojojin mata, suna tsakanin wasu motoci biyu sannan suna rera waka tare da taka rawa.

Kara karanta wannan

Tashin Hankali: An Yi Garkuwa da Matar Wani Ma'aikacin Kamfanin Mai Na Kasa NNPC

Bidiyon kyawawan sojoji mata ya ja hankalin masu kallo 415k

Dukkaninsu sun kasance sanye da kayan sojoji amma dai kansu a bude ya ke yayin da suke rike da hular sojinsu a hannu.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Dakarun sojin wadanda suka cika da farin ciki sun rera wakar 'Stand Strong' na fitaccen mawakin Najeriya wato Davido.

A daidai lokacin kawo rahoton, bidiyon ya samu fiye da mutum 415k da suka kalle shi, sannan ya samu 'likes' 27.7k da kuma martani fiye da 600.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

@Ellen Muliro ya yi martani

"Wow kun hadu."

@lawrence0034 ya ce:

"Kuna da kyau."

@Prime Nation ya yi martani:

"Haduwa, wacce nake so mai dauke da aski."

@kelvin peters ya ce:

"Naija a duniya."

@S.a.m.yahaya ya yi martani:

"Ina kaunarku yan mata."

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Jirgin Sama Cike Da Fasinjoji Ya Yi Mummunan Hatsari, Mutane Da Yawa Sun Rasu

@o.Lighty ta yi martani:

"Wow kun hadu."

@Barry ya ce:

"Dan Allah ku yan mata ku je ku yi godiya ga iyayenku mata da suka haife ku kyawawan yan mata."

@KCEEBILLIONZ ya yi martani:

"Kwamrad zo ka ga kyawawan sojoji fa."

Kyakkyawar soja ta bayyana yawan kudin da ta samu a aikin soja cikin shekara daya

A wani labarin kuma, mun ji cewa wata kyakkyawar budurwa da ke aikin soja a Amurka ta bayyana yawan kudaden da ta samu daga aikin cikin shekarar 2022.

Budurwar ta ce ta samu fiye da naira miliyan 45 a matsayin kudaden shiga wadanda suka hada da albashi da alawus dinta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel