Hoton Tsohon Zakaran Kwallon Kafa na Super Eagles, Babayaro, Tare da Iyalansa ya Kayatar
- Kyakyawan hoton tsohon zakaran kwallon kafa na Super Eagles, Celestine Babayaro, tare da iyalansa ya matukar birge masoyansa
- An kwashe shekaru ba a ji daga Babayaro inda aka dI ga rade-radin karayar arzikin da ya samu a shekarun bayan wanda yasa ya tserewa masu bin shi bashi
- A bayyanar wannan hoton tare da iyalansa, an gan shi cikin shiga mai kyau da kamalar dake fallasa irin jin dadin da yake wanda ke nuna ya fita daga mawuyacin hali
Tsohon zakaran kwallon kafa na duniya, Celestine Babayaro, ya bayyana a wani hoto mai matukar kyau da iyalansa dukkansu.
Tsohon ‘dan wasan kwallon kafan kungiyar Chelsea, a baya ya kasance daya daga cikin kwararrun masu tsaron gida da aka taba yi a Najeriya bayan bayyana da yayi a wasanni 27 a kungiyar kasa tsakanin 1995 zuwa 2004, jaridar Leadership ta rahoto.
Shekara da shekaru ba a jin duriyar Babayaro wasu suna cewa masu bin shi bashi ne suka fatattake shi saboda karayar arziki da ta same shi.
Kamar yadda rahoton Chronicle Live ya bayyana, an tattaro cewa Cele ya koma rayuwa a wani gida dake titin Laleham a Shepperton Middlesex.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A shekarar 2011, makwabtansa sun bayyana tsoronsu kan cewa tsohon ‘dan wasan kwallon kafan ya fada mawuyacin hali saboda kula da gidansa mai darajar £475,000.
Wani makwabcinsa wanda ke rayuwa a titi daya da Babayaro yace:
“Zaka iya gane cewa samun kudi yayi wuya saboda gidan a baya ana kula da shi sosai amma yanzu sai a hankali.
“Kuma ganin yadda saman ke kokarin faduwa kuma lambun duk yayi ciyayi. Sun zo sun bukaci in ara musu abun gyaran lambu amma dole ta sa na hana saboda ciyayin sun yi girma.”
A halin yanzu, an ga hoton Babayaro mai shekaru 44 wanda ‘dan uwansa Emmanuel ya wallafa, wanda shi ma shahararren ‘dan wasan kwallon kafa ne.
Cike da jin dadin masu son kwallon kafa, tsohon zakaran kungiyar kwallon kafa ta Newcastle ya bayyana shar cike da hutawa, lamarin dake nuna cewa ya girgije daga halin da ya fada a baya.
Katafaren garejin Ahmed Musa, Kyaftin din Super Eagles
A wani labari na daban, kyaftin din kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles, Ahmed Musa ya bayyana garejin motocinsa.
Ahmed Musa ya kasance ma’abocin don motocin alfarma masu matukar kyau da kayatarwa.
Asali: Legit.ng