Bayan Shekaru 9 Ana Bibiyar Mai Safarar Kwayoyi, NDLEA ta Damke Shi, Tana Neman Babban Yayansa

Bayan Shekaru 9 Ana Bibiyar Mai Safarar Kwayoyi, NDLEA ta Damke Shi, Tana Neman Babban Yayansa

  • Jami’an hukumar NDLEA sun damke wani hamshakin mai arziki wanda ya kwashe shekaru yana dillancin miyagun kwayoyi bayan shekaru 9 ana bibiyarsa
  • NDLEA tace tun 2013 take bibiyarsu shi da yayansa wanda yanzu ya tsere, an kuma kama miyagun kwayoyi lodi-lodi a gidajensu biyu a jihar Abia
  • Tare da kokarin jami’an Sojoji, NDLEA ta garkame otal dinsu, gidan cin abinc, katafaren gidajens, manyan motoci kuma ana bibiyar asusun bankunansu

Abia - Hukumar yaki da fasa kwabrin miyagun kwayoyi (NDLEA) ta damke daya daga cikin ‘yan uwa biyu da suka kasance mashahuran masu samar da miyagun kwayoyi a yankunan kudancin kasar nan.

Tambarin NDLEA
Bayan Shekaru 9 Ana Bibiyar Mai Safarar Kwayoyi, NDLEA ta Damke Shi, Tana Neman Babban Yayansa. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Kakakin hukumar, Femi Babafemi, ya sanar da hakan a wallafar da yayi a Twitter ranar Talata. Onyeaghalachi Stephen Nwagwugwu ya shiga hannun jami’an hukumar bayan shekaru tara ana bibiyarsa.

Kara karanta wannan

Abinda 'Yan Siyasar Mu Na Arewa Zasu Koya Daga 'Yan Kudu, Aisha Buhari

Kamar yadda yace, babban yayan mai suna Eze Kaleb Stephen wanda shima ake nemansa ya sha da kyar a wani samamen. Cikin dare da aka kai samamen a lokaci daya a Umuahia da Ntigha Okpuola a karamar hukumar Isiala Ngwa ta arewa dake jihar Abia.

“Bincike ya bayyana cewa manyan gagararrun ‘yan uwan sun fara harkar miyagun kwayoyi tun a shekarun 90s lokacin da suka fara matsayin kananan dillalai sannan daga baya suka kafa dabar shaye-shaye a yankinsu.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

“Daga bisani sun zama mashahuran diloli inda suka mallaki otal otal, gidaje a yankunan da suke so a jihohin Abia, Ribas da Imo tare da motocin alfarma a gidajensu.
“Tun a shekarar 2013 hukumar NDLEA take bibiyarsu a lokacin da suka shirya wani farmaki da aka kai wa jami’an hukumar da suka yi kokarin kama su a yayin wani samame. Daya daga cikin jami’an da suka kai wa harin har yanzu yana kwance yana jinya.

Kara karanta wannan

Tashin Hankali: Wata Matar Aure, Maryam, Ta Sheke Kishiyarta Kan Abu Daya a Arewa

“Manyan masu safarar kwayoyin sun mallaki tsageru dake gadin gidajensu da shagunan kwayoyi, inda suke dillancin miyagun kwayoyi kamar hodar iblis, Methamphetamine, da sauran nau’ikan wiwi.”

- Babafemi yace.

Takardar ta kara da cewa, yace sabon kokarin damke su biyun tare da gurfanar dasu ya fara ne a watanni hudu da suka wuce wanda hakan yasa aka dinga kai samame inda suke a ranar Asabar.

Babafemi yace yayin da karamin, Onyeaghalachi Stephen Nwagwugwu wanda ke zama a Umuahia babban birnin jihar Abia, aka yi nasarar cafke shi, babban yayan Eze Kaleb Stephen ya sha da kyar a lokacin da jami’ai suka dira yankin Ntigha Okpuola.

A yayin da ake samamen, daya daga cikin tsagerunsu, Eberechi Kingsley Monday, an kama shi.

Abubuwan da aka samu a gidajensu

A yayin samamen, an samu hodar iblis da wasu nau’ika na wiwi a gidajen biyu yayin da hukumar ta rufe otal dinsu biyu, gidan cin abinci, katafaran gidajensu biyu da kuma wasu manyan motocinsu yayin da ake kokarin gano asusun bankunansu da sauran kadarorinsu.

Kara karanta wannan

'Diyar Shugaban Kasa, Hanan Buhari, Ta Bude Gidauniyar Kanta Yau a Aso VIlla

Otal din da aka rufe sun hada da Jahlove, Mbawsi duk dake Isiala Ngwa ta arewa, Noycyhl otal dake babbar hanyar Aba zuwa Fatakwal, Aba da Royal Cruise Fast Food dake babbar hanyar Enugu zuwa Fatakwal duk a jihar Abia.

Buba Marwa yayi martani

A yayin martani kan wannan cigaban, shugaban hukumar NDLEA, Birgediya Janar Buba Marwa mai ritaya, ya yabawa jami’an hukumar da suke da hannu a aikin tare da sojoji da suka bayar da goyon baya.

Marwa yayi kira ga shahararren dillalin kwayoyin da ya mika kansa ga hukumar ko a zakulo shi saboda bashi da maboya.

NDLEA ta kama mai takaba da kwayoyi

A wani labari na daban, hukumar NDLEA tayi ram da wata mata mai takaba da hodar iblis a kasan takalmanta.

Matar ta yi niyyar tafiya kasar Saudi Arabia ne kuma aka damketa a filin sauka da tashin jiragen sama.

Asali: Legit.ng

Online view pixel