Hotunan da Daraja: Dankara-dankaran Motocin Dake Garejin Ahmed Musa

Hotunan da Daraja: Dankara-dankaran Motocin Dake Garejin Ahmed Musa

Fitaccen 'dan kwallon kafan Najeriya, Ahmed Musa, a cikin kwanakin nan ya saka hannu kan yarjejeniyar kwantiragin shekaru biyu da kungiyar Sivasspor bayan ya bar tsohuwar kungiyar kwallon kafa ta Fatih Karagumruk.

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Kyaftin din Super Eagles din a ranar 13 ga watan Afirilun 2021 ne ya sake shigar kungiyar Kano Pillars har zuwa karar 2020-2021.

Ahmed Musa
Hotunan da Daraja: Dankara-dankaran Motocin Dake Garejin Ahmed Musa. Hoto daga @ahmedmusa718
Asali: Twitter

Sai dai baya ga soyayyarsa ga kwallon kafa da kasarsa, zakaran 'dan wasan yana kaunar ababen hawa na kasaita kuma na zamani.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Daily Trust ta tattaro muku wasu daga cikin motocin alfarma dake garejin 'dan wasan kwallon kafan da darajarsu dogaro da wasu wallafa da yayi a soshiyal midiya.

Kara karanta wannan

Ke duniya: An kama wata malamar coci dake sayen yara kanana kan kudi N50,000

2019 Mercedes Benz V Class — (N26m – N32m)

Daya daga cikin zuka-zukan motocin dake garejin 'dan wasan kwallon kafan ita ce 2019 Mercedes Benz V class. Kamar yadda shafin yanar gizo na motoci mai suna Edbook.com ya bayyana, ta kai darajar 26m – N32m ($61,150 – $76,350).

Mercedes Benz CLS — (N31m – N33m)

Wata dankareriyar motar dake garejin kyaftin din Super Eagles din ita ce Mercedes Benz CLS. A halin yanzu ana siyar da ita kan kudi N31m and N33m ($75,150 – $77,650) kamar yadda autoblog.com suka bayyana.

2017 Porsche Macan — (N21m)

Domin mallakar wannan motar a garejin ka, dole ne mutum ya kashe N21m ($50,000) wurin siyanta kamar yadda motortrend.com ta bayyana. Wannan tana daya daga cikin motocin zakaran kwallon kafan.

Range Rover Sport — (N55m)

A 2013, 'dan kwallon ya siyawa kansa Range Rover Sport SUV wacce ta kai darajar N55m. Fitaccen yanar gizon siyar da motoci mai suna carmart.ng ya farashinta a hakan.

Kara karanta wannan

Abba Kyari Ya Magantu Kan Kadarori 14 Da FG Ta Bankado A Matsayin Nasa

Mercedes Benz G-Wagon – (N87m)

Babu shakka Mercedes Benz G-Wagon motar alfarma ce kuma duk wanda ya hau ta ya cika babban yaro a wannan zamanin.

Tana daya daga cikin motocin da gogaggen 'dan kwallon kafa Ahmed Musa ya mallaka kuma ta kai darajar N87m kamar yadda carmart.ng suka bayyana.

Ahmed Musa Ya Samu Gagarumar Cigaba, Ya Samu Shiga Kungiyar Kwallon Kafan Turkiyya ta Sivasspor

A wani labari na daban, Kyaftin din Super Eagles, Ahmed Musa, hya bar kungiyar kwallon kafan Turkiyya Fatih Karagumruk inda ya samu shiga wata gagagrumar kungiyar mai suna Sivasspor a yarjejeniyar shekaru biyu.

Zakaran 'dan wasan kwallon kafan wanda ya kwashe shekara daya a Karagumruk ya yanke hukuncin barin kungiyar ne domin ya gangara Sivasspor.

An tattaro cewa, Kocin Riza Calimbay ne ya bukaci karbar matashin 'dan kwallon mai shekaru 29 a duniya kuma sun gana a ranar Alhamis da ta gabata.

Kara karanta wannan

Akalla Kudi ₦462 Za'a Fara Siyar Da Litan Mai Idan Aka Cire Tallafi Bayan Zaben 2023, NNPC

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel