Kasar Senegal Za Ta Yi Hayar ’Yan Tsubbu Domin Yiwa Mane Magani

Kasar Senegal Za Ta Yi Hayar ’Yan Tsubbu Domin Yiwa Mane Magani

  • Dan wasan kasar Senegal, Sadio Mane na kan ganiyar rasa damar shiga wasan cin kofin duniya da za a yi a Qatar
  • Senegal ta ce za ta yi amfani da malaman tsubbu don tabbatar da tura Mane kasar Qatar don buga wasannin
  • Rahoto ya bayyana yadda Mane ya samu rauni a kafa yayin bugawa Bayern Munich wasa da abokiyar gwabzawarta Werder Bremen

Senegal - Kasar Senegal za ta yi amfani da malaman tsubbu wajen warkar da Sadio Mane a kokarin da kasar ke yi na tura dan wasan ya buga mata wasan cin kofin duniya a kasar Qatar.

An ruwaito cewa, kasar ta saka Mane a cikin jerin 'yan wasanta da za su buga wasan cin kofin duniya duk da kuwa ciwon da ya ji a kafarsa a makon nan, Daily Mail ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: ASUU ta magantu kan za ta fara sabon yajin aiki ko kuma za ta ci gaba da aiki

Wata majiya ta bayyana cewa, wannan batu na fitowa ne daga mahukunta a fannin kwallon kafan kasar ga jaridar AFP a ranar Alhamis.

Senegal za ta yi amfani da malaman tsubbu wajen warkar da Sadio Mane
Kasar Senegal za ta yi hayar Bokaye domin yiwa Mane jinyar rashin lafiya | Hoto: si.com
Asali: UGC

Kasar Senegal ya shiga tashin hankalin rashin Mane a filin wasan kofin duniya, wanda a cewar majiya hakan babban kalubale ne.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Za mu yi duk mai yiwuwa mu kawo Mane filin kofin duniya

Amma a yanzu, Fatma Samoura, ta biyu a shugabannin kwallon kafa ta duniya ta ce, kasar za ta yi duk mai yiwuwa domin tabbatar da bayyanarsa a filin wasa.

Ta kuma bayyana cewa, ba a san dai ta yaya ba, ko kuma aiki da 'yan tsubbu zai ba da fa'ida, amma dai za su gwada tare da fatan ganin mu'ujizar da ke ciki.

A cewar Fatma ga Europe 1:

"Za mu yi amfani da malaman tsubbu, ban sani ba (ko suna da tasiri) amma a wannan lokacin, duk da haka za mu yi amfani dasu. Muna fatan ganin mu'ujiza. Dole ya kasance a can."

Kara karanta wannan

Allah ya yiwa wani babban jigon tawagar kamfen Atiku a Abuja rasuwa

Yadda Mane ya samu rauni

Dan wasan na Bayern Munich ya fita daga filin wasa mintuna 15 da farwa yana dingishi yayin da kulob din ke gwabzawa da Werder Bremen a makon nan, EuroSport ta ruwaito.

Duniyar kwallon kafa ta shiga yada batun cewa, wannan rauni da Mane ya samu zai zama masa sanadin rasa damar shiga gasar cin kofin duniya da za a yi a Qatar.

Shugaban Munich, Julian Nagelsmann ya tabbatar da jin raunin Mane, kana ya bayyana cewa, za a yi gwaji domin duba kafar tasa.

Hakazalika, ya ce za a duba yiwuwar ko ciwon zai iya barinsa ya buga wasannin cin kofin duniya da aka sa a gaba.

Ba Sadio Mane kadai ba, a baya mun kawo muku jerin sunayen 'yan wasan da ba za su samu daman buga wasannin cin kofin duniya ba saboda raunuka da suka samu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.