Shahararren ‘Dan Kwallon kafan Najeriya Ya Koma Jami’a, Yana Neman Ilmin Digiri
- ‘Dan wasan Super Eagles, Wilfred Ndidi ya kammala wani kwas da yake yi domin samun kwarewar kasuwanci a jami’ar Birtaniya
- Wilfred Ndidi ya samu shaidar karatu daga De Montfort University a Leicester wanda za ta ba shi damar yin digiri da digir-gir
- Wannan yana cikin dabaran ‘dan kwallon kafan Najeriyan na neman kudi ko da ya yi ritaya daga buga wasan kwallo a nan gaba
United Kingdom - ‘Dan wasan kwallon kafan Najeriya, Wilfred Ndidi ya kammala karantun da yake yi a jami’ar De Montfort da ke Leicester a Ingila.
Vanguard a rahoton da ta fitar kwanaki ya bayyana cewa Wilfred Ndidi ya samu shaidar yin kwas a fannin kula da kasuwanci a jami’ar Birtaniyar.
Da aka zanta da shi a Football Daily, ‘dan kwallon na kungiyar Leicester City ya bayyana cewa ya kammala kwas da yake yi a jami’ar ta De Montfort.
Babu Kudi A Harkar Fim: Jarumin Fim Ya Nemi EFCC Da NDLEA Su Binciki Jarumai Maza Da Ke Siyan Manyan Gidaje
“Kwarai (Na ji dadin shi). Na kammala. Na yi kwas na kimanin darasi 10 da za su bani damar samun digiri da kyau a jami’a.”
“Saboda in waye a kan ilmin kasuwanci da neman kudi da kuma yawan shakatawa ne kurum.”
- Onyinye Wilfred Ndidi
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Shirin ritaya
Wannan ilmi da ‘dan wasan kwallon kafan ya samu zai taimaka masa sosai musamman bayan ritaya, domin ‘yan kwallo ba su karbar fansho.
‘Yan wasan kwallon kafa su na fuskantar kalubale da zarar sun daina buga tamula. Wannan kwas zai bude idon Ndidi wajen neman kudi nan gaba.
Ndidi ya ci ribar zaman Ingila
Ndidi ya zo Ingila ne bayan da Leicester City ta saye shi daga kungiyar KRC Genk a 2017. A 2019 ya fara karatu a jami’ar De Montfort da ke Birtaniya.
Legit.ng Hausa ta fahimci ‘dan wasan na Super Eagles yana cikin ‘yan wasan tsakiyan da ake ji da su a gasar Firimiya saboda yadda ya iya tare.
Jaridar Daily Post tace kafin yanzu an yi ‘dan wasan Najeriya, Seyi Olofinjana wanda ya yi digiri a jami’ar fasaha ta Ladoke Akintola sa’ilin yana Najeriya.
Daga baya Olofinjana ya yi digiri na biyu a jami’ar Aberdeen University a lokacin shi ma yana bugawa kungiyar Wolverhampton Wanderers kwallon kafa.
Yajin-aiki a Najeriya
Dazu ne aka ji wasu jami’o’in Jihohi na komawa aiki bayan barazanar Gwamnoni na tsaida albashinsu kamar yadda Gwamnatin Tarayya tayi alwashi.
Malaman Jami'ar GSU za su daina karbar albashi idan suka yi sake, sannan shugaban jami’ar EKSU yace za su cigaba da karatunsu daga yau.
Asali: Legit.ng