Ronaldo ya na neman yin kwantai, kungiyoyi 5 sun ki sayen ‘Dan wasan Man Utd
- Akwai jita-jitan Cristiano Ronaldo yana neman kai da Man United ko kungiyar yana neman kai da shi
- Jorge Mendes wanda shi ne Dillalin Cristiano Ronaldo, ya dage wajen samun masu sayen ‘dan wasansa
- An cigaba da yada cewa ‘Dan wasan gaban zai tashi daga kulob dinsa, shekara daya da barinsa Italiya
England - Cristiano Ronaldo yana neman rasa kungiyar da zai bugawa kwallon kafa yayin da ake ta rade-radin yana neman barin Manchester United.
Sports Brief ta kawo rahoto manyan kungiyoyin Turai irinsu Paris Saint Germain da Bayern Munchen sun ki yarda su dauki hayar ‘dan wasan gaban.
Cristiano Ronaldo mai shekara 37 a Duniya yana neman barin Manchester United ne zuwa kungiyar da ta ke buga wasa a gasar kofin nahiyar Turai.
Shekara daya da dawowarsa Ingila, ‘Dan wasan na kasar Portugal ya fara neman mafita. Wasu kuma su na cewa sabon koci ne bai da bukatarsa.
Rahoton da ya fito daga Daily Trust ya bayyana cewa ana tunani Bayern Munich za su dauki gwarzon ‘dan wasan ganin Robert Lewandowski zai tashi.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Jaridar Sports Bible ta jero kungiyoyin da suka ki yarda su saye Cristiano Ronaldo kamar haka:
1. Bayern Munich
Dillalin tauraron Jorgen Mendes ya tuntubi Bayern Munich da niyyar su dauki Cristiano Ronalo, sai aka ji Oliver Kahn yana cewa ‘dan wasan bai dace da tsarinsu ba.
2. Paris Saint Germain
Haka zalika akwai rade-radin an yi wa Paris Saint Germain tayin Ronaldo har abin ya kai an ji Lionel Messi yana yabonsa. Amma PSG ta nuna ba za ta hada taurarin Duniyan ba.
3. Barcelona
Wani rade-radi mai ban mamaki da alaman nisa da gaskiya shi ne Jorge Mendes ya je Sifen, ya nemi ya tallatawa Barcelona tsohon abokin gaban na su a lokacin yana Madrid.
4. Chelsea
Maganar zuwan Tauraron zuwa Chelsea ya yi nisa kamar yadda The Guardian ta rahoto dillalinsa ya zauna da Todd Boehly, amma Thomas Tuchel ya nuna bai da bukata.
5. Man City
Wasu abokan gaban da aka nemi a tallatawa Ronaldo su ne Manchester City. Akwai maganar tun 2021, amma har yanzu magana ba tayi karfi a kan daukar ‘dan wasan ba.
Ronaldo ya yi rashi
Idan aka rabu da kwallon kafa, za a tuna cewa daya daga cikin jariran da Budurwar Cristiano Ronaldo watau Georgina Rodriguez ta haifa, ya mutu.
Cristiano Ronaldo ya sanar da wannan a Instagram, ya bukaci mutane su ba su dama su wartsake. Mun fitar da wannan labari a watan Afrilun 2022.
Asali: Legit.ng