Saboda budurwa: Fitaccen dan kwallon Arsenal ya tabbatar da karbar addinin Muslunci
- Thomas Partey ya bayyana cewa dalilin da ya sa ya musulunta shi ne, yana matukar son budurwarsa ‘yar kasar Morocco
- Da yake bayar da karin bayani, dan wasan tsakiyar na Ghana ya tabbatar da cewa babu bambanci tsakanin addinan biyu
- Thomas yana magana ne yayin wata tattaunawa ta yau da kullun da 'yar jaridar kafar watsa labarai Nana Aba Anamoah
Ghana - A karshe dai mataimakin kyaftin din kungiyar kwallon kafa ta maza ta Ghana, Black Stars, Thomas Partey, ya tabbatar da jita-jitar da ake yadawa na cewa yanzu ya Musulunta.
A wata ‘yar gajeriyar hira da Nana Aba Anamoah, Thomas ya bayyana cewa ya yanke shawarar sauya addini ne saboda yana kaunar budurwarsa kuma babu bambanci tsakanin Kiristanci da Musulunci.
A cewarsa:
"Ina da yarinyar da nake so, na san 'yan matan kodimo na za su rabu da ni amma ba matsala ... Na girma tare da Musulmai don haka a karshen dai abu daya ne."
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Abin da 'yan Ghana ke cewa
Sorkpor Che Tsatsu yayi sharhi da cewa:
"Zai kare cikin kuka. Ba kirista bane. Ka cika fom ne kawai don neman addini da Kiristanci. Babu Kirista na gaskiya da ya sadu da yardar Allah da zai iya canja yakini. Wani abu ne mu zama Kirista kuma wani abu ne daban mu sadu da yardar Allah da za ta canja rayuwarka gabaki daya."
Zedkizzy ya ce:
"Kai ne ya kamata ka mai da ita addininka a matsayinka na mai gida, domin kai kake jagoranta yayin da ta ke bi. Ina addu'ar kada ta mulke ka."
Teboh Junior ya ce:
"Har yanzu "buduwarka" ce kawai . Kuma ka musulunta saboda ita. Don haka bari mu kalli batun ta wannan gefen, a ce mutum kamar kai har yana da nasa ra'ayin.
"Idan abubuwa ba su yi kyau tsakaninsu ba, za ka sake sauya addini ne??? Kuma ka tuna cewa addini kira ne na ruhaniya ba kawai kowane irin gayyata ba . Ka daina shiga da fita a addinai na mutanena.
Haka kawai a saci abu na: Mawaki ya caccaki APC bisa kunna wakarsa a zaben fidda gwani
A wani labarin, tauraron mawaki, Timi Dakolo, ya bayyana bacin ransa tare da nuna rashin jin dadinsa ga jam’iyyar APC mai mulki da ta yi amfani da wakarsa ta Great Nation a lokacin babban taronsu na zaben fidda gwanin dan takarar shugaban kasa.
Segalink ne ya jawo hankalin Timi kan yadda APC ta yi amfani da wakar, inda ya tambaye shi ko an biya shi kudin wakarsa?
Segalink ya yada yadda aka kunna wakar kuma ya tambaya cewa: "Dan uwana Timi Dakolo ina fatan za a biya mu wannan waka da ake yi a babban taron jam'iyyar APC? Great Nation."
Asali: Legit.ng