Likitan CAF Ya Yanke Jiki Ya Faɗi Bayan Wasar Najeriya Da Ghana, Akwai Yiwuwar a Hukunta Najeriya
- Najeriya na iya fuskantar hukunci bayan wani likitan da aka hada da kungiyar tarayya ta kwallon kafar nahiyar Afirka ya fadi ya mutu a filin wasan Abuja
- Ba a san asalin abinda ya janyo mutuwar likitan ba, ta yuwu mutuwar Allah da Annabi ya yi, ko kuma mutane ne suka yi sanadi
- Bayan an hura usur din karshe, fusatattun matasa sun afka filin inda suka janyo rikici da hayaniya a cikin filin wasan kwallon
Abuja - Wani likita da ke aiki da kungiyar wasan kwallon kafar nahiyar Afirka, CAF, Dr. Joseph Kabungo ya mutu jim kadan bayan Ghana ta cire Najeriya a gasar kwallon kafa da aka yi ranar Talata, 29 ga watan Maris.
Kabungo, likita ne dan asalin kasar Zambia, kuma ya mutu ne bayan wani cunkosu ya auku a filin wasan Moshood Abiola da ke Abuja kafin a fara wasan, Legit.ng ta rahoto.
Sai dai wani rahoto ya nuna yadda likitan ya mutu sakamakon yadda mutane suka afka filin wasan da yawansu.
The Punch ta ruwaito cewa har yanzu daga jami’an kungiyar wasan kwallon kafar Najeriya har na CAF babu wadanda suka tabbatar da mutuwar likitan.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
FIFA ta yi magana akan yadda mutane suka cunkushe a filin wasan Abuja
BBC ta ruwaito yadda kungiyoyin kwallon kafa na kasa da kasa za su yi dubi akan abubuwan da suka auku a filin wasan da ke abuja kuma zasu bukaci bayanai daga jami’an tsaro da kuma ma’aikatan kwallon kafar Najeriya.
Fusatattun ‘yan kallo sun dinga jifan ‘yan wasan kwallon da robobin ruwa, wanda hakan yasa suka dinga rufe kawunansu yayin da suke kokarin barin filin.
Shugaba Muhammadu Buhari yana cikin manyan bakin da suka mara wa ‘yan kungiyar wasan kwallon kafar Najeriya akan ‘yan kungiyar wasan ta kasar Ghana.
Asali: Legit.ng