Da Duminsa: Tottenham ta naɗa sabon koci awanni 24 bayan raba gari da Nuno Espirito

Da Duminsa: Tottenham ta naɗa sabon koci awanni 24 bayan raba gari da Nuno Espirito

  • Kungiyar kwallon kafa ta ƙasar Ingila, Tottenham Hotspur, ta sanar da ɗaukar sabon koci, Antonio Conte, har zuwa ƙarshen kakar wasa 2023
  • Wannan dai na zuwa ne awanni 24 bayan ƙungiyar ta raba gari da tsohon kocinta Nuno Espirito, wanda ya sha ƙashi a hannun Man United
  • Sabon koci, Conte, ya nuna matukar jin daɗinsa bisa dawowa fagen tamaula kuma da ƙungiyar daje buga Premier League, wato Tottenham

London - Ƙungiyar kwallon ƙafa Tottenham Hotspur ta sanar da naɗa Antonio Conte a matsayin sabon mai horar da yan wasanta.

Punch tace wannan sanarwa ta zo ne awanni 24 kacal bayan ƙungiyar ta sallami tsohon kocinta, Nuno Espirito Santo.

Antonio Conte
Da Duminsa: Tottenham ta naɗa sabon koci awanni 24 bayan raba gari da Nuno Espirito Hoto: @Antonio Conte
Asali: Facebook

Channels tv tace Tottenham ta sanar a shafinta:

"Muna farin cikin sanar da cewa mun naɗa Antonio Conte a matsayin sabon koci, a kan kwantiragi har zuwa ƙarshen kakar wasanni ta 2023, da zaɓin tsawaita zamansa."

Kara karanta wannan

Gwamnatin tarayya ta karbi bashin N8.29 trillion cikin kudin yan fansho dake ajiye a banki

Jawabin sabon koci

Da yake jawabi bayan cimma yarjejeniya da ƙungiyar, Conte yace:

"Ina matukar farin ciki da dawowa ta harkar horarwa, kuma a ƙungiyar dake fafata gasar Premier Leagues na ƙasar Ingila."
"Tottenham Hotspur tana da filin wasa ɗaya daga cikin mafi kyau a duniya, na ƙagu in fara aikin jagorancin tawagar yan wasa, da kuna soyayyar magoya bayanta."

Jawabin daraktan Kwallon kafa na Tottenham

Da yake tsokaci kan naɗin sabon koci, daraktan kwallon kafa na ƙungiyar ta Tottenham Hotspur, Fabio Paratici, yace:

"Muna maraba da zuwan Conte ƙungiyarmu, tarihin da ya kafa a fagen tamaula kaɗai ya isa ya bayyana waye shi, yana da kwarewa daban-daban kuma ya ɗaga kofuna anan Ingila da kuma Italiya."
"Nasan nasarorin da Conte zai iya kawo mana, kasancewar na yi aiki tare da shi a Juventus, kuma mun ƙosa mu ga ya fara aiki tare da zaƙaƙuran tawagar yan wasan mu."

Kara karanta wannan

Tashin Hankali: Wata Budurwa ta mutu jim kadan bayan ta kwana a dakin saurayinta

Barca ta sallami kocinta

A wani labarin kuma Kungiyar Barcelona ta raba gari da mai horad da yan wasa, Ronald Koeman

Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ta sallami mai horad da yan wasanta, Ronald Koeman, bayan ta sha ka shi a hannun Rayo Vallecano.

Barcelona ce ta sanar da haka a shafinta na yanar gizo, bayan rashin nasarar da ta yi, ya maida ita mataki na 9 a teburin gasar Laliga ta kasar Spain.

Asali: Legit.ng

Online view pixel