Albashin ma'aikata
Ministar harkokin mata Hajiya Imaan Sulaiman-Ibrahim, ta bayyana cewa ba ta rike kowane ma'aikaci a zuciya ba kan zanga-zangar da suka gudanar a kanta.
Likitoci masu neman kwarewar aiki ssun sanar da shiga yajin aiki tare da rufe asibitocin gwamnati da ke a fadin Najeriya kan rashin cika alkawarin gwamnati.
Kungiyar ma'aikatan kananan hukumomi watau NULGE ta koka kan rashin fara biyan ma'aikatan kananan hukumomi albashin N70000 a Kaduna, Borno da Gombe.
Gwamnatin jihar Bauchi ta gano ma'aikatan bogi a fannin lafiya. Hukumar kula da asibitocin jihar ta bayyana matakin da za a dauka kansu kan cin amanar da su ka yi.
Kungiyar likitoci masu neman kwarewar aiki, ta tsunduma yajin aikin gargadi na kwanaki 7 a birnin tarayya, kan rashin biyan albashi, karancin ma'aikata da sauransu
Kungiyar kwadago ta kasa (NLC), ta bayyana cewa mafi karancin albashin da ake biyan ma'aikata ya yi kadan. Ta bukaci gwamnati ta yi gaggawar sake duba shi.
Gwamnoni da dama sun haura dokar mafi karancin albashin Najeriya watau N70,000, jihar Imo ce a sahun gaba bayan Uzodinma ya yi kari zuwa N104,000.
Gwamnatin Abia ta sallami ma'aikata shida daga aiki bayan bincike ya gano yadda suka yi magudi a tsarin biyan albashi, suka rika karbar kudi fiye da hakkinsu a wata.
A labarin nan, za a ji cewa gwamnatin tarayya ta bayyana yadda ta ceto wadansu jihohi 27 na kasar nan daga matsalar gaza biyan albashin ma'aikata.
Albashin ma'aikata
Samu kari