Albashin ma'aikata
NLC ta ce sai an duba yanayin rayuwar yau wajen yanke mafi karancin albashi. Joe Ajaero ya ce tun da Ibrahim Badamasi Babangida ya fito da tsarin SAP ake wahala.
Gwamna Abba Kabir na jihar Kano ya kaddamar da biyan kudaden 'yan fansho dubu biyar a jihar har naira biliyan shida da kuma kudaden giratutin ma'aikata.
Gwamnan jihar Abia Alex Otti ya sanar da shirin karin mafi karancin albashi ga ma'aikata a jiharsa. Gwamnan zai kuma biyar yan fansho kudaden da suke bin bashi.
Gwamnan Zamfara, Dauda Lawal, ya bayyana shirin gwmanatinsa na biyan waɗanda suna ritaya hakkokinsu na gratuti da fanshi waɓda suka biyo tun daga 2015.
Mafi karancin albashi a yau N30, 000 ne, zuwa Maris babu wanda za a biya wannan kudi.Gwamnati ta ce nan da 'yan watanni kadan sabon tsarin albashi zai soma aiki.
Tsofaffin ma’aikatan da su ka yi ritaya za su je gidan gwamnatin jihar Kano da karfe 9:00 na Asabar dauke da takardunsu domin a tantance su saboda a biya fansho.
Sabon shugaban ma'aikatan jihar Kano, Musa Abdullahi ya gargadi ma'aikatan jihar da su guji zuwa wurin aiki a latti inda ya kafa musu lokacin zuwa aiki.
Wani dan Najeriya da ke aiki a matsayin dan agaji ya baje kolin makudan kudaden da yake samu a kullun bayan kula da wani tsoho. Ya ce aikin na ci sosai a Birtaniya.
Gwamnatin jihar Kano ta gano wasu daliban makarantar sakandire (JSS da SSS) a cikin ma'aikatan jihar. An kuma gano masu bautar kasa da dan shekara 13 a ciki.
Albashin ma'aikata
Samu kari