Kudu maso gabashin Najeriya
Hukumar ƴan sandan farin kaya (DSS) ta yi bayanin cewa har yanzu shugaban ƴan aware na ƙungiyar IPOB, Nnamdi Kanu yana tsare, kawai likitoci ne suka duba shi.
An shiga jimami biyo bayan mutuwar manyan alƙalai biyu na Najeriya. Mai shari'a Chima Nweze da na kotun ƙoli da Peter Mallong na babbar kotun tarayya sun mutu.
An samu hargitsi sosai da asarar rai a lokacin da jami'an gwamnatin jihar Imo, suka ƙona wasu shaguna da matsugunan Hausawa a wasu kasuwanni guda uku na jihar.
Babban bokan nan na jihar Anambra da ƴan bindiga suka tasa ƙeyarsa, Chukwudozie Nwangwu, ya bayyana dalilin da ya sanya ya bari ƴan bindiga suƙa tafi da shi.
'Yan sanda sun tabbatar da sakin shahararren boka Chukwudozie Nwangwu da masu garkuwa suka sace a dakin otal a Anambra a safiyar yau Asabar 29 ga watan Yuli.
Wani lauya a birnin Tarayya, Abuja, Emmanuel Ekwe ya yi barazanar maka tsohon gwamnan jihar Ebonyi, Dave Umahi a kotu idan har bai karbi mukamin minista ba.
Kwamishinan kasuwanci da masana'antu na jihar Abia ya tsallake rijiya da baya a wani mummunan hari da ƴan bindiga suka kai masa a tsakiyar birnin Aba na jihar.
Jamia'an 'yan sanda sun bazama neman wasu da ake zargin sun sace wani kasurgumin Boka a jihar Anambra, an rasa rayuka yayin sace bokan a dakin otal din shi.
Ƴam bindiga sun bi tsakar dare sun yi awon gaba da wani babban boka mai bayar da maganin bindiga a jihar Anambra. Ƴan bindigan sun sace shi ne a otel ɗinsa.
Kudu maso gabashin Najeriya
Samu kari