Jihar Sokoto
Ana hasashen wasu gwamnonin jihohin Najeriya za su iya samun matsala a zaben 2027 da ke tafe saboda matakan da suka dauka daban-daban a jihohinsu.
Malamai a Arewacin Najeriya sun bayyana cewa, ba za su amince ba a taba martabar Sakin Musulmi alhali suna kallo. Sun bayyana matsayarsu kan ci gaba da mulkin.
Gwamnan jihar Sokoto, Ahmed Aliyu Sokoto, ya gargadi jami'an gwamnati da suka karkatar da kudaden goron Sallah da aka ba ma'aikata da su mayar da su.
Gwamna Ahmed Aliyu na jihar Sokoto ya tube sarakuna akalla 15 bayan hawansa karagar mulkin jihar tare da kirkirar sabuwar doka da za ta rage ikon Sultan.
Alhaji Muhammad Abubakar Sa'ad III, sarkin Musulmi da ke Sokoto, ya bayyana cewa ya shirya tsaf domin bin duk wata doka da gwamnatin jihar Sokoto za ta gindaya.
Gwamnatin jihar Sokoto ta bayyana cewa mai alfarma Sarkin Musulmi bai da ikon nada kowa a idon doka. Ta ce hakan ya sanya za ta yiwa doka gyara a jihar.
Fadar Sarkin Musulmi ta fito ta yi magana kan batun rikicin da ake yadawa tana yi da gwamnatin Sokoto. Fadar ta ce babu wata rigima a tsakanin bangarorin biyu.
Yayin da ake kokarin gyaran fuska a dokar masarautun jihar Sokoto, yau Talata za a fara sauraran ra'ayin jama'a game da sabuwar dokar da ake magana a kai.
Rikicin sarauta da ake fama da shi a Kano ya kai wani mataki da ya samar da sarakuna biyu - Sarkin da aka tube amma ya ki amincewa da hakan, kuma batun na kotu.
Jihar Sokoto
Samu kari