Siyasar Najeriya
Duk da kokarin Bola Tinubu kan sulhunta rikicin Nyesom Wike da Siminalayi Fubara abin ya ci tura bayan sake nada sabon shugaban Majalisar jihar a yau.
Binciken gano gaskiya da aka gudanar kan hoton da ake yaɗawa cewa Yahaya Bello ya yi shigar ƴan Daudu ya gano cewa ba tsohon gwamnan bane a hoton.
Tsohon dan takarar majalisar wakilai a karkashin inuwar jam'iyyar African Democratic Congress (ADC) a jihar Abia ya sauya sheka zuwa jam'iyyar APC.
Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta yi hukunci kan shirin da PDP ke yi na tsige shugabanta na kasa, Umar Damagun. Kotun ta haramtawa jam'iyyar daukar wannan mataki.
Gwamna Siminalayi Fubara na jihar Ribas ya haramtawa dukkan ciyamomin jihar da jagororin kananan hukumomi su shure gayyatar zuwa majalisar dokoki.
Wani jigo a jam’iyyar APC Mohammed Saidu Etsu ya shigar da kara kotu yana neman kotu ta dakatar da Abdulahi Ganduje daga shugabancin jam'iyyar baki daya.
Tsohon kwamishina a jihar Kano, Musa Ilyasu Kwankwaso ya yi iƙirarin cewa tun kafin hukuncin kotun ƙoli aka cimma matsaya da Gwamna Abba Kabir zai baro NNPP.
A cikkn kwanaki kalilan da suka gaba, jam'iyyar PDP a jihar Abia ta rasamanyan kusoshi ciki har da tsohon kakakin majalisar dokokin jihar da tsofaffin mambobi.
Jam'iyyar APC reshen jihar Ribas ta umurci majalisar dokokin jihar ta fara shirin tsige Gwamna Siminalayi Fubara daga kan madafun iko ba tare da ɓata lokaci ba.
Siyasar Najeriya
Samu kari