
Haduran mota a Najeriya







Rundunar 'yan sanda ta fara farautar wani tirelan mota da ya murkushe jami'in karbar haraji a Legas. An ce direban ya tsere ya bar motarsa a kan babbar hanya.

Wata tanka makare da iskar gas ta kife a jihar Katsina, inda ta aka ga wuta ya na tashi bayan fankar ta fashe tare da kamawa da wuta wanda ya jawo asara.

An kara samun hadarin tankar mai a Jigawa. Tankar mai ta sake kamawa da wuta amma an kashe wutar ba tare da jawo asarar rayuka ko dukiyar al'umma ba.

Wani jami'in dan sanda ya rasa ransa bayan wani hatsarin mota ya ritsa da shi a jihar Legas. Dan sanda ya rasu ne bayan ya makale sakamakon hadewar wasu motoci.

Tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ziyarci jihar Jigawa domin jaje bayan hadarin tankar man fetur. Buhari ya ba da tallafi Naira miliyan 10 a Jigawa.

Wata motar haya da ta kuccewa direba ta daki bakin gada, ta faɗa kogi a karamar hukumar Njaba da ke jihar Imo, duka fasinjojin cikin motar sun kwanta dama.

Allah ya yi wa tsohon mataimakin kakakin majalisar dokokin jihar Kwara, Hon Christopher Ayeni rasuwa sakamakon wani mummunan hatsari da ya rutsa da shi.

Wani dan acaɓa ya rasu bayan karo da ya yi da tirelar Dangote a jihar Legas. Motar kamfanin Dangote ta markaɗa ɗan acaɓan har lahira yayin da suka yi karo.

Wasu sojojin saman Najeriya sun gamu da hatsarin mota yayin sa suke kan hanyar zuwa babban birnin tarayya Abuja. Sojoji biyar sun kwanta dama a hatsarin.
Haduran mota a Najeriya
Samu kari