Rabiu Kwankwaso
Mun ji Kwankwaso yace Jam’iyyar APC ta karbe duk abubuwan da su ke da shi amma ba ayi masu sakayya da komai ba bayan zaben 2019. Tsohon Gwamnan da yake magana game da siyasar 2019 yace wannan ya sa su ka koma PDP.
Mai Girma Sanata Kwankwaso Ya Kai Ziyara Gidan Marigayi Sheikh Isyaka Rabiu Domin Yiwa iyalansa Gaisuwa, ya ziyarci Iyalan Marigayi ‘Dan Masanin Kano da kuma Bashir Tofa da ma fadar Mai martaba Sarki Muhammadu Sanusi II.
Mun ji cewa Rabiu Kwankwaso ya shigo Kano domin ganin PDP ta sha kasa a 2019 inda Surukin sa zai yi takara da Ganduje. Kwankwaso yana cikin wadanda su ka nemi takarar Shugaban kasa a Jam’iyyar PDP amma ya sha kashi.
A jiya Jam’iyyar PRP ta canza ‘Dan takarar Gwamna a Jihar Kano inda Takai ya samu tikitin takarar Gwamna bayan ya doke Farfesa Hafiz Abubakar da kuma Sanata Isa Yahaya Zarewa da irin su Kabiru Muhammad Gwangwazo, da Aminu Nabegu.
Za ku ji cewa Abokin Takarar Atiku Abubakar a PDP ya gana da Kwankwaso inji wani babban Hadimin Sanatan. Yanzu haka dai ana ta cigaba da kulle-kullen tika Jam’iyyar APC da kasa a zaben 2019 a Jam’iyyar adawa ta PDP.
Malam Ibrahim Shekarau wanda ya taba yin Gwamna a Jihar Kano yayi hira da wata Jaridar inda yayi magana game da yadda zaben 2019 za ta kasance yace saboda a zauna lafiya a Jihar Kano ya fasa takara a PDP ya koma APC.
Za ku ji Jam’iyyar PRP ta fara janyewa Kwankwasiyya da kuma Jam'iyyar PDP Mabiya a Jihar Kano bayan shigan Malam Salihu Sagir Takai wanda ya bar PDP bayan an ba Surukin tsohon Gwamnan Jihar Kano Abba Yusuf takara
Majiyar LEGIT.com ta ruwaito a kwanakin baya ne dai aka samu rahotanni dake nuna PDP ta tsayar da Takai a matsayin dan takararta na gwamnan jahar Kano a zaben 2019, duk da cewa jam’iyyar ta gudanar da zaben fidda gwani kuma suruki
Za ku ji abin da Mawallafin Bidiyon zargin Ganduje ya bayyanawa Majalisa jiya da aka gayyace sa. Yanzu ma dai an mikawa Majalisa kundin Bidiyoyin cin hancin Gwamnan Kano inda ya rika karbar makudan Dalolin Amurka.
Rabiu Kwankwaso
Samu kari