Kamfanin wutar lantarkin Najeriya
Matsalar wutar lantarki a yankin Arewa maso Gabas ya kara ƙamari yayin da mutanen yankin suka bukaci Ministan makamashi, Adebayo Adelabu ya yi murabus.
Asusun bada lamuni na duniya (IMF) ya bukaci shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya kammala cire tallafin man fetur da lantarki da zarar an gama raba tallafin kudi.
Shugaban kungiyar ta NLC a Kogi, Kwamred Gabriel Amari ya bayyana karin kudin wuta da fashi da makami kan talakawan Najeriya. Ya bayyana haka ne a yau.
Kungiyar kwadago ta yi barazanar rufe ofisoshin kamfanonin raba lantarki a fadin kasar nan, har sai gwamnatin tarayya ta janye karin kudin wutar.
Kungiyoyin kwadago na NLC da TUC sun rufe hedikwatar hukumar kula da wutar lantarki (NERC) da kuma ofisoshin kamfanonin rarraba wutar lantarki a fadin kasar.
A yayin da wa'adin da kungiyoyin kwadago ta ba hukumar NERC ya kare, mambobin NLC da TUC sun fara rufe ofisoshin kamfanin rarraba wutar lantarki da ke fadin Nigeria.
Kamfanin rarraba hasken wutar lantarki na KEDCO ya ce ana shirin kara karfin wutar lantarki d ake samarwa a jihohin Kano, Jigawa da Katsina domin inganta wutar.
Kungiyar kwadago ta yi barazanar fara zanga-zanga a fadin Najeriya idan gwamnati bata janye karin kudin wuta da ta yi ba zuwa ranar Lahadi, 12 ga watan Mayu
An shiga jimami a unguwar Gama B dake jihar Kano bayan an tsinci gawar wani magidanci, Bello Bukar Adamu a karamar hukumar Kumbotso da ya bar gida ranar Lahadi.
Kamfanin wutar lantarkin Najeriya
Samu kari