Kamfanin wutar lantarkin Najeriya
Kamfanin rarraba hasken lantarki na kasa (TCN) ya ce za a cigaba da samun matsalar rashin wuta har na tsawon lokaci kafin ya dawo yadda ya dace a kasar nan.
Ministan wutar lantarki, Adebayo Adelabu, ya umarci a gaggauta gyara tashar wutar lantarki, yayin da kamfanin TCN ya gargadi cewa tashar wutar na iya sake lalacewa
'Yan Najeriya sun yi martani yayin da tashar wutar lantarki ta sake durkushewa a karo na biyu cikin kwanaki uku. Durkushewar ta yau ita ce ta 11 a cikin 2024.
Rahotanni na nuni da cewa tushen wutar lantarkin Najeriya ya kara lalacewa yayin al'umma suka kara shiga duhu. hakan ya faru ne sau biyu a kwanki uku.
A wannan rahoton za ku ji yadda kamfanonin rarraba hasken lantarki (DisCos) sun sanar da kara kudin lantarki da ake biya ta mita da abokan huldarsu ke amfani da su.
Gwamnatin tarayya ta ce ta gano matsalar da ke jawo yawan lalacewar wutar lantarki a Najeriya bayan kasa ta sake fadawa duhu a karo na 10 a shekarar 2024.
Mazauna Arewacin kasar nan su ka shiga mawuyacin hali bayan shafe fiye da rabin Oktoba babu wutar lantarki wanda ya jawo asarar akalla Naira tiriliyan 1.5.
Kamfanin TCN ya fara dawo da wuta a Abuja bayan lalacewar tushen wutar lantarki na kasa. TCN ya ce sannu a hankali zai maido wutar a dukkan jihohi.
Rahotanni sun bayyana cewa tashar wutar lantarki ta sake durkushewa karo na 10 a cikin shekarar 2024. Durkushewar tashar ya sake jefa Najeriya a cikin duhu.
Kamfanin wutar lantarkin Najeriya
Samu kari