Ogun
Dakarun ‘yan sanda a jihar Ogun sun kubutar da wani mutum da aka yi garkuwa da shi. Wannan mutumi ya ga ta kan sa tun da aka yi damfara, amma ya dauke kudin.
Yan sanda sun kama wasu masu damfara ta yanar gizo wato yan yahoo da suka yi garkuwa da abokin aikinsu kan zarginsa da rashin basu kasonsu cikin N22m na zamba.
Hukumar kashe gobara ta jihar Legas da Ogun sun tabbatar da tashin wata gobarar cikin dare a fitacciyar kasuwar Ajimula dake tsakanin iyakokin Ogun da Legas.
Wasu mutane sun dauki mara lafiyarsu sun kai asibiti cikin tsakar dare, aka yi rashin sa'a ba tayi rai ba. A kan wannan wani uba da yaronsa suka zane ma'aikata.
Wasu mahara da ake zaton Fulani makiyaya ne sun aika wasika zuwa wasu kauyuka hudu a yankin karamar hukumar Yewa da arewa a jihar Ogun, sun ce zasu kai hari.
Mutane shida ‘yan gida daya sun sheka lahira bayan cin abincin dare wanda ake kyautata zaton tsaka ce ta shiga cikin miyar kuma suka ci suka koshi a jihar Ogun.
Babbar kotun tarayya mai zama a babban birnin tarayya Abuja ya jaddada halascin zaben fidda gwanin Jam'iyar PDP da ya samar da Oladipupo Adebutu a jihar Ogun.
John Obeta, wani matashi dan shekara 27 dan asalin jihar Enugu, wanda ake zargi da kashe budurwarsa mai suna idowu Buhari ya ce kudinsa ne aka tura asusunta.
Kotun daukaka kara dake zama a jihar Ogun, ta yi watsi da hukuncin wata kotun tarayya da ta soke zabukan fidda gwanin jam’iyyar PDP na jihar inda tace kure ne.
Ogun
Samu kari