Ana Neman Matar Da Ta Kona Kishiyarta Da Wuta Ruwa A jallo

Ana Neman Matar Da Ta Kona Kishiyarta Da Wuta Ruwa A jallo

  • Kishi kumallon mata, wata mata ce ta bankawa kishiyarta wuta wadda tayi sanadiyar zuwanta barzahu
  • Mata dai na nuna tsananin kishinsu ga matan da mazajen su suka aura ko kuma matan da suke kulawa
  • A Nigeria ana yawan samun ire-iren wannan fitunannun mata sun kashe mazajensu ko kuma sun kashe budurwa ko abokiyar zamansu

Instablog9ja masu wallafa a shafin Twitter sun wallafa wasu hotuna boyu masu auke da abin ta'ajibi da kuma mamaki.

Hoto na farko hoton wasu mata ne guda biyu, daya daga bangaren dama, daya kuma daga bangaren hagu.

Na bangaren daman hotan wata mata ce da aka wallafa hotan wata mata ba dankwali tana murmushi a kasan kuma an rubuta wani rubutu kamar haka

"Ana neman wannan matar da ake zargi ta kona kishiyarta har lahira a Owerri"

Kara karanta wannan

Bidiyon Zabgegiyar Damisa Tana Takun Isa Cikin Jama'a Da ke Shakatawa ya Janyo Cece-kuce

Daya matar kuwa ta jikin wannan hotan ta ne tsaye ne sanye da kayan bikin da kuma dan kwali a kanta.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kashe mata
Ana Neman Matar Da Ta Kona Kishiyarta Da Wuta Ruwa A jallo Hoto: Instablog9ja
Asali: Twitter

To sai dai daya hotan da ya ja hankali kuma shine yadda aka ga Nwwnneka Ifunrunwa ya wallafa wata magana yana mai cewa

"Wannan hotan yar uwatace da kuke gani wadda kishiyarta ta sa mata wuta ba dan komai ba sai dan tsananin kishi, kamar yadda kuke gani rundunar yan sandan suna nemanta ruwa a jallo

Masu amfani da kafar Twitter sun bayyana ra'ayoyinsu game da wannan batu

Sakamakon wannan ba shi ne farau ba, da yawan mutane kan tofa albarkacin bakinsu kan irin wannan abun al'ajabin.

@thewiseone98 cewa yace

"Har wayau, yar kabilar Igbo ce"

@i'mdeji shi kuwa a nasa ra'ayin cewa yace

Kara karanta wannan

Yadda Hannun Gajeruwar Yar Bautar Kasa Ya Gaza Kaiwa Saman Allo, Dalibai Sun Fashe Da Dariya a Bidiyo

"Ya kamata a kama mijin ma"

shi kuwa @findingkin cewa yace

"matan kabilar Igbo sun fara tsoratani"

Wata mata ta kashe mijinta da taffassashen ruwan zafi

Wata mata Ramma Soliu ta kashe mijinta da tafassashen ruwan zafi a unguwar Fulani dake yankin iyana Ilewo a dake karamar hukumar Abekuta ta arewa a jihar Ogun.

Jaridar Tribune ta rawaito cewa matar sun shafe kusan shekaru 6 da mijin nata kuma suna diban soyayya, wadda har ta kai ga samun yaya ma a tsakani.

A rawaiton dai an ce mijin na cin amanar matar tasa ne, wanda dalilin haka yasa ta yanke hukuncin hakan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel