Ogun
Shugaban hukumar NYSC ya yi nuni da cewa matasa masu yiwa kasa hidima za su amfana da sabon mafi karancin albashi. Ya nuna cewa za a yi musu karin alawus.
Kimanin matafiya 20 ne rahotanni suka ce wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da matafiya a kan hanyar Sagamu-Ijebu-Ode a ranar Lahadi da misalin karfe 9 na dare.
Rikici ya barke tsakanin masu nadin sarki a yankin Ofe da ke karamar hukumar Ose a Ondo inda suka koka kan yadda ake kokarin ƙaƙaba musu wani a matsayin sarki.
Kungiyar gwamnonin Kudancin Najeriya ta bukaci ba jihohi damar biyan abin da za su iya game da mafi karancin albashi da kungiyar kwadago ke nema cikin kwanakin nan.
Gwamnonin jihohohin kudancin Najeriya su 17 suna tattaunawa a jihar Ogun a yau Litinin. Wannan shi ne taron su na farko tun bayan rasuwar gwamnan jihar Ondo.
Gwamna Dapo Abiodun na jihar Ogun ya tabbatar da dokar da za ta dakile sarakunan gargajiya shiga duk wata yarjejeniya da ta shafi filaye a fadin jihar.
Sarkin masarautar Akinale a jihar Ogun, Oba Olufemi Ogunleye ya riga mu gidan gaskiya bayan fama da gajeruwar rashin lafiya a asibitin Landan ranar Laraba da yamma.
Oba Abdurrashid Akanbi na Iwo dake jihar Ogun ya ce bai yi nadamar karya gunki mai shekaru 800 a fadarsa ba kuma zai cigaba da riko da addinin Musulunci a rayuwarsa.
Hukumar kiyaye hadura ta kasa FRSC ta sanar da cewa hadarin mota ya yi sanadiyyar mutuwar mutane biyu a jihar da jikkata da dama. Florence Okpe ce ta sanar.
Ogun
Samu kari