Sarkin Kano
Shugaban jam'iyyar APC na kasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya musanta rahotannin da ke cewa yana da hannu a shirin da ake yi na tsige Sanusi II.
Abba Kabir Yusuf ya yi alkawarin gina gidaje kyauta a dukkan kananan hukumomin Kano ga wadanda suka shiga ambaliyar ruwa. Abba ya ce hakan zai rage radadi.
Kotun majistare a jihar Kano ta sake tasa keyar matashin dan jarida zuwa gidan gyaran hali na Kurmawa kan zargin cin mutuncin Gwamna Abba Kabir da Sanusi II.
Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero, ya nuna alhininsa kan ambaliyar ruwan da ta auku a jihar Borno. Ya yi addu'ar Allah ya jikan wadanda suka rasa rayukansu.
Babbar kotun jihar Kano da ke zamanta a birnin Kano ta hana Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero daga yin gyara a fadar Sarkin da ke Nasarawa a cikin Kano.
Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero ya gayyaci Musulmi zuwa bikin Maulidin Annabi Muhammad (SAW) a gobe Asabar 14 ga watan Satumbar 2024 a fadarsa.
Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya roki al'umma addu'o'i domin ubangiji ya hada kan attajiran jihar guda biyu, Aliko Dangote da Abdussamad Rabiu domin samun cigaba.
Sarkin Potiskum da ke jihar Yobe, Mai Martaba, Umar Bauya ya kai ziyarar goyon baya ga Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II a jihar inda ya roke shi alfarma.
Za a ji cewa mutane da yawa suka rasu a Najeriya a watan Satumban nan na 2024. A ciki akwai Dada Yar’adua, Alhaji Idris Bayero da mawakin nan Garba Gashuwa.
Sarkin Kano
Samu kari