Yan wasan Kannywood
Jarumi a masana'antar Kannywood, Sadik Sani Sadik ya ce yana fim ne ba don koyar da tarbiyya ba, illa neman kuɗi kawai saboda tarbiyya daga gida ake samu.
Jarumar Kannywood, Rahama Sadau ta bayyana abubuwan da ke burgeta a kan mai martaba Muhammadu Sanusi bayan sun yi wata haduwar ba zata a filin jirgin sama.
Shahararren jarumin fina-finan Kannywood, Abubakar Waziri ya ce da ba ya harkar fim, da ya zama malamin addini saboda yana da sha’awar gyaran al’umma.
Fitaccen jarumin Kannywood, Mustapha Badamasi Nabraska ya sauya sheka zuwa APC bayan fita daga NNPP da Kwankwasiyya a hannun Sanata Barau Jibrin a Abuja.
Hukumar tace finafinai ta Kano ta dakatar da Samha M. Inuwa da Soja Boy bisa laifin tsiraici da batsa a bidiyo, tare da kwace lasisinsu. Mun yi bayani kan jaruman.
Jarumar Kannywood, Maryam Malika, ta runtuma kotun Shari’a da ke Magajin Gari, Kaduna domin neman a tabbatar da sakin da tsohon mijinta mai suna Umar ya yi mata.
Kamfanin man Najeriya na NNPCL ya shirya hadaka da jaruman Kannywood kan wayar da kan 'yan kasa. Ya zauna da Rahama Sadau, Hadiza Gabon da sauransu.
Bayan kalaman Usman Soja Boy kan shirya fina-finai a masana'antar Kannywood, furodusa Abdulaziz Dan Small ya kalubalanci mawakin kan alfaharin da ya yi.
Masu kallo sun roƙi a cire Firdausi Yahaya daga shirin Jamilun Jiddan, duk da haka ta zama fitacciya a fina-finai da ta samu kambun "Jaruma Mai Tasowa."
Yan wasan Kannywood
Samu kari