Yan wasan Kannywood
Hukumar tace finafinai ta Kano ta dakatar da jarumar Kannywood, Samha M. Inuwa, na shekara guda saboda hotuna da bidiyo na batsa da suka tada hankali.
Jaruma Radeeya Jibril ta yi aure, ta gode wa wasu 'yan masana'antar finafinan, tana mai alfahari da Kannywood, kuma ta nemi yafiya ga duk wanda ta yiwa ba daidai ba.
Rahama Sadau da Umar M Shareef sun taka rawa a Kaduna don murnar sabuwar shekara. Bidiyonsu ya jawo martani masu dadi, inda jama'a ke musu addu’a da fatan alheri.
Matar mawaki Ado Gwanja, Maryam, ta haifi ɗa namiji mai suna Nawab. Mutane sun taya su murna tare da addu’ar Allah ya raya yaran cikin Musulunci.
An samu ci gaba sosai a harkar finafinan Hausa a shekarar 2024 da ta gabata. Legit Hausa ta zakulo wasu finafinai 5 da suka yi tashe a shekarar da ta gabata.
Allah ya yiwa mahaifiyar marigayi Ahmad S Nuhu rasuwa. Shugaban hukumar fina finan Najeriya, Ali Nuhu ya sanar da lokacin da za a yi mata jana'iza a Jos.
Mawaka irinsu Sadiq Saleh, Ado Gwanja, da Umar M Shareef sun yi fice a 2024 da wakokinsu na soyayya, al'adun Hausa, da kuma salon da ke sanya rawa a gidajen biki.
Ali Nuhu ya gargadi jaruma Rayya kan yunkurin da take yi na zana tattoo. 'Yan Kannywood da dama sun mara masa baya, suna neman ta dakatar da wannan shiri.
Hassan Giggs ya gode wa Hadiza Gabon bisa abubuwan alherin da ta rika yi masa, yana yabawa kaunarta ga iyalinsa da jajircewarta a masana'antar Kannywood.
Yan wasan Kannywood
Samu kari