Jami'o'in Najeriya
Shugaban kasa Bola Tinubu ya nada mutane 61 mukamai a majalisun gudanarwan manyan makaratun Najeriya 36 yayin da yake murnar cika shekara 2 da hawa mulki.
Kungiyar malaman jami'o'in Najeriya watau ASUU ta yi barazanar tsunduma yajin aiki matukar gwamnatin tarayya ba ta cika mata alkawurran da ta ɗauka ba.
Yan Najeriya sun nuna takaici kan yadda ɗalibai suka faɗi jarabawar share fagen shiga jami'o'i da sauran manyan makarantu watau UTME, sun tattaro dalilai.
Wani dan sanda ya saki wuta a wurin bincike ababen hawa a jihar Benuwai, harsashi ya yi ajalin wata daliba da ke ajin karshe a jami'a ranar Juma'a.
JAMB ta ce ɗalibai 379,997 daga jihohi 6 za su sake rubuta UTME bayan kuskure a sakamakon jarabawar, yayin da WAEC ta amince za ta taimaka a sake jarabawar.
Majalisar Wakilan tarayya ta yanke shawarar gudanar da bincike kan tangarɗar na'ura da aka samu yayin tantance sakamakon dubban ɗaliban da suka zana UTME 2025.
Sakamakon kura-kuran fasahar na'ura da aka samu, sama da dalibai miliyan ɗaya da rabi suka kasa samun sama da maki 200 a UTME 2025. JAMB ta dauki mataki.
Za ku ji cewa jami’ar Maryam Abacha ta rufe dakunan kwanan dalibai mata biyu a Kano bisa zargin lalata da kin bin doka, tare da gargadi ga dalibai da iyayensu.
Rikici ya barke a jami'ar Katsina kan zaɓen VC. 'Yan takara sun soki zaɓen, sun zargi shugaba mai barin gado da nuna son zuciya domin wanda yake so ya samu nasara.
Jami'o'in Najeriya
Samu kari