Fadar shugaban kasa
Karamin ministan kwadugo da samar da ayyukan yi a gwamnatin Buhari, Festus Keyamo, ya ce ikon Allah ne kaɗai zai iya kawo cikas a bikin rantsar da Asiwaju.
Ministan birnin tarayya Abuja, Mallam Muhammed Bello, ya ce ya yi nadama na gaza jawo hankalin Sanatan ɗaya a Abuja ya sauya sheka daga PDP zuwa APV kafin zaɓe.
Rahotanni daga babban birnin kasar Mali, sun nuna cewa harin kwantan ɓauna ya yi ajalin shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa da wasu manyan mutane huɗu.
A yau ake jin an aika takarda zuwa ga SGF da ta nuna Asiwaju Bola Tinubu ya fitar da sunayen mutanen da za su taya shi aiki wajen karbar ragamar mulki a Mayu.
Shugaba Buhari ya nuna takaicin sa kan rikicin da ya ɓarke a ƙasar Sudan, shugaban ƙasar ya yi kiran da ɓangarorin biyu da su tsagaita wuta su hau teburin sulhu
Mai magana da yawun shugaban ƙasa, Femi Adesina, ya ce idan har za'a tsaya a yi zancen gaskiya dole a yaba wa shugaba Muhammadu Buhari game da matsalar tsaro.
Fadar shugaban ƙasa ta bayyana cewa gwamnati mai ci ta samu koma baya lokacin da shugaba Muhammadu Buhari ya kwanta rashin lafiya tsawon watanni 8 a Landan.
A ranar Jumu'a, limamin masallacin da ke cikin gidan gwamnati ya rufe karatu da fassara Alkur'ani sakamakon zai tafi kasa mai tsarki, Saudiyya gudanar da Umrah.
An fahimci cewa wasu wadanda Bola Tinubu yake jin shawararsu, sun dage Sanusi Lamido Sanusi watau Muhammadu Sanusi II ya koma kan kujerarsa na Gwamnan CBN.
Fadar shugaban kasa
Samu kari