Hukumar Sojin Najeriya
Dakarun rundunar sojin Najeriya sun samu galama mai girma a yaƙin da suke da ƴan bindiga a kananan hukumomin Birnin Gwari da Chikun a jihar Kaduna.
Dakarun sojoji da haɗin guiwar ƴan sanda sun samu nasarar ceto ƴan bautar ƙasa biyu duk mata daga hannun 'yan bindiga a jihar Katsina ranar Alhamis.
Babban hafsan tsaron kasar nan, CDS Christopher Musa, ya ce sojoji na tare da mulkin Demokutaɗiyya, don haka kowa ya kwantar da hankalknsa kan juyin mulki.
Rundunar sojin Najeriya da hukumar DSS sun yi nasarar dakile mummunan harin 'yan 'yan ta'addan Boko Haram a karamar hukumar Gezawa da ke jihar Kano.
Luguden wutan jirgin yaƙin sojin Najeriya na rundunar Operation Haɗi Kai ya yi sanadin mutuwar mayakan Boko Haram sama da 160 a jihohin Yobe da Borno.
Tsageru ɗauke.da muggan makamai sun kai farmaki har cikin gida, sun yi awon gaba da shugaban ma'aikatan shugaban majalisar dokokin jihar Adamawa.
Rahotanni sun bayyana cewa ana zaman makokin kisan matasa 17 da Boko Haram ta yi a jihar Yobe, wank ya sake tashi da masu zuwa jana'iza, an rasa rayuka 20.
Rundunar sojoji a jihar Kebbi ta yi ajalin wani kasurgumi kuma kwamandan 'yan bindiga, Mainasara da wasu biyu a jihar Kebbi a wani mummunan hari da ta kai.
Rahotanni sun bayyana cewa tsohon shugaban ƙaramar hukumar Ukum a jihar Benuwai, Raymond Erukaa, ya rasu a hannun masu garkuwa da mutane inji ɗansa.
Hukumar Sojin Najeriya
Samu kari