Labaran tattalin arzikin Najeriya
Babban bankin ƙasa watau CBN ya karyata labarin da ake yaɗawa a kafafen sada zumunta cewa za a fara amfani da sababbin takardun Naira 5,000 da N10,000.
Kasashen Mali, Nijar da Burkina Faso sun kakaba harajin kashi 0.5% kan kayayyakin da ke shigowa daga mambobin kasashen ECOWAS ciki har da Najeriya.
Bankin duniya ya amince da ba gwamnatin Najeriya bashin kudi har dala miliyan 500 domin habaka tattali. Za a raba kudin ne wa 'yan kasuwa da gidajen jama'a.
Shugaban kasa, Bola Tinubu ya fadi yadda ya yi barazanar korar Minista Nyesom Wike idan manufofinsa ba su dace da bukatun jam’iyyar APC mai mulki ba.
Minista Wike ya raba buhunan shinkafa 10,000 ga addinai da makarantu a Abuja don Ramadan, inda shugabanni suka gode, suna cewa zai taimakawa mabukata.
Tsohon minista a Najeriya, Sheikh Isa Ali Pantami ya gargadi shugabanni daga kan kansiloli har shugaban kasa da su tabbata sun yi adalci ga al'ummar da suke mulka.
Kunguyar CDD ta yi kira ga shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya ƙaƙaba dokar ta ɓaci a jihar Zamfara saboda dalilan karya doka da tattalin arziki.
NAFDAC ta kama buhuna 120 na jabun shinkafa a Rivers, inda ta kai su ofishinta na Kudu maso Kudu, ta kuma kama wata mata tare da kayan hada jabun shinkafar.
Kasuwar hada-hadar ta NGX ta fuskanci koma baya, inda masu hannun jari suka tafka asarar N1.4tn. Duk da haka, masana na ganin dama ce ta sayen hannun jari da araha.
Labaran tattalin arzikin Najeriya
Samu kari