Labaran tattalin arzikin Najeriya
Dattijon dan siyasa, Alhaji Tanko Yakasai ya jaddada goyon baya ga manufofin gwamnatin tarayya, tare da bayyana cewa ba a ware Arewa daga cin gajiyar shirin ba.
Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya ce an fara ganin haske kan yadda lamura suka fara daidaita. Ya ce shekaru 50 da suka wuce an gaza daukan matakan da suka dace.
Ministan sadarwa, Mohammed Idris ya ce sauye-sauyen da ake yi suna haifar da sakamako mai kyau, yana mai yabawa hakurin ‘yan Najeriya da kira ga kara addu’o’i.
Babban bankin Najeriya watau CBN ya bullo da sabon tsarin da za a riƙa ɗaukarwa ƴan Najeriya kudi idan suka yi amfani da ATM suka cire N20,000 ko sama da haka.
Gwamnatin Najeriya ta sanya hannu kan kafa sabon kamfanin siminti a jihar Kebbi. Kamfanin zai samar da aiki ga mutane 45,000 idan aka kammala shi a jihar.
Yayin da farashin abinci ya fadi a watan Ramadan, tsohon mai ba da shawara na shugaban ƙasa, Reno Omokri, ya yabi shugaba Bola Tinubu saboda faduwar darajar kaya.
Gwamnatin jihar Katsina ta samar da rumbun sauki domin karya farashin abinci ga talakawa. Za a rika sayar da abinci a Funtua, Daura da Katsina a yanzu.
Gwamnatin Kogi ta fara karɓar harajin GR daga masu filaye. Amma ba za a biya haraji kan gine-ginen gwamnati, wuraren ibada, asibitoci, da makarantu ba.
Babban bankin Najeriya (CBN) ya sanar da nada sababbin darektoci da aka dora wa alhakin kula da bangarori daban-daban da zummar kara habaka ayyukan bankin.
Labaran tattalin arzikin Najeriya
Samu kari