Labaran tattalin arzikin Najeriya
An shawarci 'yan Najeriya da su fara tanadin abinci da rage kashe kudi yayin da ake shirin shiga shekarar 2024 wacce ka iya zuwa da matsin rayuwa.
Fitaccen faston Najeriya, Primate Elijah Ayodele ya bayyana cewa farashin shinkafa yar waje zai kai N80,000 kan kowani buhu a cikin shekarar 2024.
Za a fahimci cewa binciken da Jim Obaze ya yi game da abubuwan da su ka faru a bankin CBN a lokacin Godwin Emefiele ya fallasa abubuwa a mulkin Muhammadu Buhari.
Kwararru a harkar tattalin arziki sun nuna shekarar 2024 za ta zo da sauki. Tun da Bola Ahmed Tinubu ya hau mulki yake dambe da tattalin arzikin Najeriya.
An gano Gwamnonin da su ka zama ci-ma-zaune a Najeriya. Za a ga jihohin da za su tsaya da kafafunsu da wadanda za su ruguje idan aka janye FAAC a Najeriya.
Jagoran APC, Hon. Olatunbosun Oyintiloye ya ce magani ya fi karfin ‘Yan Najeriya, sai shugaban kasa ya yi wani abu. ‘Dan siyasar ya yi kira ga Bola Ahmed Tinubu.
Kudin Najeriya; Naira sun kara daraja a kasuwar musayar kudi ta duniya biyo bayan dogon kai ruwa rana da aka yi a baya na darajar kudin kasar ta Afrika.
Dangote ya samu kishiya a kasuwnacin matatar man fetur, BUA zai fara harkar a jihar Akwa Ibom a nan ba da dadewa ba, bayani ya fito daga wata mata.
Kamfanonin waje za su zo da kudi su yi kasuwanci a kasar nan. Masana suna ganin hakan zai samar da ayyukan yi ya kawowa gwamnati kudin shiga a 2024.
Labaran tattalin arzikin Najeriya
Samu kari