Hukumar yan sandan NAjeriya
Wasu 'yan bindiga dauke da makamai sun kai hari kan jami'an 'yan sanda a jihar Enugu. 'Yan bindigan sun hallaka mutum hudu a yayin mummunan harin da suka kai.
'Yan bindiga dauke da makamai sun kai harin ta'addanci a jihar Benue. 'Ƴan bindigan sun hallaka mutane bakwai tare da raunata wasu da dama yayin harin.
Rahotanni sun bayyana cewa tsohon shugaban riƙo na karamar hukumar Talata Mafara da tsohon kansila na cikin waɗanda aka kashe a harin garin Morai a Zamfara.
Tsohon gwamnan Kano kuma jagoran NNPP na ƙasa, Dr. Rabiu Musa Kwankwaso ya yi Allah wadai da harin da ƴan bindiga suka kashe gomman mutane a Filato.
Wasu miyagun ƴan bindiga sun farmaki wurin ibada a lokacin da mutane ke tsakiyar bautar Ubangiji a tsaunin Lokoja, sun sace mutane da dama da daddare.
Bayan shirya yin garkuwa da manyan mutane, wani shahararren dan bindiga, , Chumo Alhaji daga Babanla, ya mutu bayan ya kamu da ciwon farfadiya a Kwara.
Rundunar yan sandan jihar Anambra ta bayyana cewa an cafke wani mutum mai shekaru 49 da ake zargi da hallaka mahaifiyarsa saboda sabani a kan kudin kasuwancin rogo.
Umar Sule, wani dattijo dan sheka 50 da ke Bauchi ya amsa laifin dirka wa 'yarsa ciki. Rundunar 'yan sanda na shirin mika shi gaban kotu bayan kama shi.
Rundunar 'yan sandan Najeriya ta bayyana ta sanar da cewa ta samu nasarar gano wata kungiya da ke safarar mugayen makaman da ake kera wa a cikin kasar a jihar Kano.
Hukumar yan sandan NAjeriya
Samu kari